‘Yan ta’addar da su ka kama ƙananan yara 39 a Katsina sun nemi a biya su Naira miliyan 30 kafin su sake su.
Sun bayyana cewa su na so su yi magana da mai gonar da su ka kama yaran a gonar sa.
Sun yi alƙawarin ba za su saki yaran ba, har sai an biya masu buƙatar su ta biyan su fansar Naira miliyan 30.
An kama yaran a wata gona a Mairuwa, cikin Ƙaramar Hukumar Faskari, amma kusa da Funtuwa.
Wasu daga cikin yaran ‘yan cikin ƙauyukan Funtuwa ne, wasu kuma daga ƙauyukan ƙaramar hukumar Faskari.
PREMIUM TIMES HAUSA ta ji daga majiya mai tushe cewa ‘yan ta’addar sun mamaye gonar a ranar Asabar da rana tsaka, su ka kwashi masu aikin gona sama da 40. Cikin waɗanda aka tafi da su ɗin, yara 39 ƙanana ne, kuma sun kasa tserewa.
Majiyar ta ce maharan sun tuntuɓi wasu daga cikin iyayen yaran, inda su ka nemi sai an biya su naira milyan 30 kafin su sake su.
“Mai gonar bayan nan lokacin da aka yi awon-gaba da yaran, sai wani mai kula da gonar mutum ɗaya. Sun kira iyayen yaran su ka ce masu ba za su karɓi ƙasa da abin da su ka nemi a biya su ba. Ko kuma a haɗa su da mai gonar.
“Sun ce sun yi ƙwaƙƙwaran bincike sun gano cewa mai gonar attajiri ne. Saboda haka yanzu sun ce lallai sai an haɗa su da mai gonar.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Katsina ya ce su na sane da lamarin.
Discussion about this post