Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya kare matsayar bijirewar da su ka yi wa Atiku shi da gwamnoni huɗu ‘yan G5.
Wike ya ce ai abin da su ka yi wa Atiku yanzu, wato sharuɗɗan da su ka gindaya kafin su amince da Atiku, cikin cokali zuwane idan aka kwatanta da tsauraran sharuɗɗan da Atiku ya gindiya wa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, lokacin da Atiku ɗin ya yi masa tawaye a 2015.
Babban gogarman G5 Wike ya bayyana irin abin da ya kira ‘rashin mutuncin’ da Atiku ya yi wa Jonathan, lokacin da Jonathan ɗin ya tsaya takara a zaɓen 2015. Wike ya yi bayanin lokacin da yake buɗe wani titin da gwamnatin sa ta gina. Gwamna Dave Umahi na Ebonyi ne ya taya shi buɗe titin.
Wike ya ce, “Jonathan ya na shugaban ƙasa, amma ya yi tattaki har otal ɗin Dorchester a Landan, ya iske Atiku. Amma Atiku “ya tozarta” shi. Ya ce masa sai dai ya sauka daga takarar shugabancin ƙasa a PDP, ya bar wa Atiku ɗin.
“Wato shi ɗan Adam akwai shi da saurin manta tarihi. Cikin 2015 lokacin Jonathan ya na shugaban ƙasa, kuma ɗan takara, kuma har ya ci zaɓen fidda-gwani, sai ya je ya samu Atiku har Landan, ya roƙe shi ya dawo PDP ya goya wa Jonathan ɗin baya.
“Sai Atiku ya ce masa sai fa idan shi Jonathan ɗin zai sauka daga takarar shugabancin ƙasa a PDP ɗin ya bar masa. Kamar Atiku wai zai kalli idon shugaban ƙasa da ke kan mulki, kuma ya ci takara, amma ya ce masa wai ya sauka ya bar masa takarar.
Matsayar Mu A Yau:
“Mu kuma a yau ba fa cewa mu ka yi Atiku da ke takarar shugaban ƙasa ya sauka daga takara ba. Ba son ran mu ne mu ka nuna ba. Kawai cewa mu ka yi tunda kai ne ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, to mu ma a bai wa wani daga cikin mutanen mu shugabancin jam’iyya, a wuce wurin.” Inji Wike.
Discussion about this post