A cikin bayanan da ɗan majalisa Ado Doguwa yayi wa BBC Hausa da shima Murtala Sule-Garu ya ti kan ainihin abin da ya faru a wajen taron APC a Kano dukkan su sun ƙaryata juma da suke bayanin ainihin abin da ya faru.
Ado Doguwa ya ce bai wawuri kofin da mataimakin gwamnan ke shan shayi a wurin taron ya rankwala wa Garu ba, santsi ya kwashe shi a lokacin da ake cacan baki ya yanke jiki ya faɗi kasa sharaf, ya fasa bakin sa.
Doguwa ya ce bai jefe shi da kofin shayi ba.
Amma kuma da ya ke bayani a nasa ɓangaren, Sule-Garu ya ce sam ba haka a ka yi ba.
Ya ce ” Alokacin da cacan baki ya kaure tsakani na da Doguwa wanda kokari ne nayi don in nuna masa cewa ƙorafe-ƙorafen da yake yi ba gaskiya bane, sai ya fusata ya wawuri kofin shayin da ke gaban mataimakin gwamna ya jefe ni da shi.
A karshe dai Doguwa ya gargaɗi APC da shi kansa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya rike duka ƴaƴan jam’iyyar a matsayin ƴaƴan sa, ya daina nuna wasu ƴaƴan Bowa ne wasu kuma ƴaƴan Mowa.
Shi dai Doguwa ya rika yin korafi ne cewa ba a tafiya da shi a tafiyar wannan kamfen da ake ciki.
” Kowa ya san irin ƙarfin da ƙwankwaso ya ke dashi a jihar Kano, a haka muna tare ma yaya aka ƙare ballantana ana samun irin wannan ɓaraka a jam’iyyar?” In ji Doguwa.
Discussion about this post