Wasu cikakkun ‘yan ta-kife sun bi daren Laraba, kafin wayewar garin Alhamis, su ka banka wa ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) wuta, a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
Wakilin mu da ya garzaya ofishin da ke kusa da Iyaka ‘Mortuary’, ya samu cikakken bayanin cewa ‘yan ta-kifen waɗanda su uku ne, sun yi riƙa jiƙa sunƙin biredi cikin fetur, su na wurgawa a ofishin, sannan su ka ƙyasta wuta su ka tsere.
Mai gadin ofishin mai suna Azeez Hamzat, ya shaida wa wakilin mu cewa bayan an banka wutar, ya yi gaggawar kiran ‘yan sanda.
Majiya ta tabbatar wa wakilin mu cewa wasu kayayyaki da dama sun ƙone ƙurmus kafin jami’an kashe gobara su kai ɗauki.
Wakilin mu ya gano daga cikin ofisoshin da su ka ƙone, akwai ɗakin ajiyar kayayyaki, Ɗakin Yin Rajista, Zauren Shirya Taruka da sauran wasu wurare.
Kwamishinan Zaɓe na Jihar Ogun, Niyi Iyalaye ya tabbatar wa wakilin mu da wannan lamari da ya ce abin mamaki da takaici ne matuƙa.
“Amma dai yanzu mun kai rahoto wurin ‘yan sanda, kuma su na bincike,” inji shi.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya ce bai san da labarin ba, saboda bai ƙarasa ofis ba tukunna. Amma idan ya ƙarasa ya natsu, zai yi ƙarin bayani.
Discussion about this post