Sufeto Janar Usman Alƙali Baba ya bayyana cewa Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi jarimin mutum ne da ya tashi haiƙan ya kakkaɓe gaggan masu laifi a jihar sa.
Ya ce ba za ka taɓa jin Gwamna Yahaya Bello ya na ƙorafin cewa ba shi ne ke kula da jami’an tsaro a jihar sa ba.
Sufeto Janar Alƙali ya ce idan ana maganar samar da tsaro, Yahaya Bello ya yi rawar gani, a yaƙi da matasa masu ɓatagari masu aika manyan laifuka.
“Ni dai ban taɓa jin Gwamna Yahaya Bello ya fito ya yi ƙorafin cewa jami’an tsaro da ke jihar ba a hannun sa su ke ba. Saboda shi ya na iya ƙoƙarin sa na yin aiki tare da ba su haɗin kai, kuma shi ke shiga gaba domin samar da tsaro.
“Yawancin laifukan da ake ganin ‘yan jihar Kogi na aikatawa, to ba a cikin jihar su ke aikata irin laifukan ba.
Da ya ke jawabi, Bello ya ce ya samu nasarar sa a fannin tsaro da taimakon gwamnatin sa da kuma haɗin kan jami’an tsaro, har ma ya a ce a ranar 8 Ga Fabrairu, 2017 ya karɓi kyautar yabo ta Gwarzon Musamman na Inganta Tsaro, wadda tsohon Sufeto Janar Ibrahim Idris ya damƙa masa.
Ya ce ita ce kyauta irin ta ta farko da aka taɓa bai wa Gwamna daga Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.
“Haka ma a ranar 26 Ga Disamba, 2020, Manjo Janar MG Ali tsohon Kwamandan Zaratan Sojojin Musamman ya jinjina wa irin ƙoƙarin da na taɓa yi.
Discussion about this post