Ministan Harkokin Ilmi Adamu Adamu, ya nuna takaici da da-na-sanin yadda ma’aikatar sa kasa kawar da yara ƙanana masu gararamba kan titi ba su zuwa makaranta.
Ya ce ya yi baƙin cikin kasa cimma wannan buri duk kuwa da cewa ya shafe fiye da shekaru bakwai ya na Ministan Ilmi.
Adamu ya yi wannan takaici ne a lokacin da ya ke jawabi wurin buɗe taron Majalisar Gudanarwar Ilimi ta Ƙasa.
An dai fara taron ne tun a ranar Litinin a Abuja, kuma za a rufe a ranar Juma’a.
“Tun da na hau matsayin Ministan Harkokin Ilmi, na shawarci gwamnonin Najeriya cewa a kafa dokar-ta-ɓaci kan matsalolin ilmi, musamman a matakin farko, wato ‘yan firamare, amma gwamnonin su ka ƙi amincewa.
A lokacin da Adamu ya zama Minista a 2015, ƙididdiga ta nuna cewa akwai yaran da ta ke watangaririya kan titi ba su zuwa makaranta har miliyan 10.5.
A yanzu kuma ana raɗe-raɗin cewa sun ma nunka, musamman idan aka yi la’akari da irin ɓarnar da ‘yan bindiga su ka shafe shekaru su na yi a yankunan karkara, inda kacokan al’ummar yankin sun dogara ne da makarantun gwamnati.
Hakan ya ƙara haifar da kulle makarantu a garuruwa da ƙauyuka da dama a Arewa maso Yamma da wasu yankuna da dama.
Irin yadda ‘yan bindiga da dama ke yawan afkawa makarantu su ka yin garkuwa da ƙananan yara, ya haifar da koma baya sosai wajen ilmi a matakin farko.
Sannan matsin rayuwa da ƙuncin talauci ya maida yara ƙananan da dama mabarata, wasu kuma ya tilasta su fita kullum yin aikin ƙarfi domin ciyar da kai.
Ƙananan yaran da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda su ka kashe iyayensu yawanci duk sun yi bankwana da karatun zamani.
Adamu ya ce saboda tunda gwamnoni su ka ƙi yarda a kafa dokar-ta-ɓaci kan matsalar ilmi a matakin farko, ya kasance babu wani hoɓɓasa da zai iya yi, domin alhakin inganta ilmi a matakin farko ya rataya ne a wuyan gwamnonin jihohi, ba Gwamantin Tarayya ba.
Discussion about this post