Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, ya bai wa dukkan magoya bayan APC abin da ya kira laƙanin kariyar sukar shekaru, ilimi, zargin rashawa da tikitin Muslim-Muslim da ake yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu.
Da ya ke jawabi a gangamin APC a Legas, wanda aka yi ranar Asabar a filin wasa na Teslim Bologon a Legas, Gbajabiamila ya bayyana cewa a yanzu a ƙasar nan babu mashahurin ɗan siyasar ci gaba kamar Tinubu.
Ya ce Tinubu gwarzon ɗan siyasa ne, wanda ya gina shugabanni da dama a matakan mulki ko shugabanci daban-daban, su kuma su ka zama wani abu har su ka gina al’umma, su ka gina ƙasa.
Da ya koma kan surutan rashin sanin takamaimen adadin shekarun Tinubu a duniya, Gbajabiamila ya ce, “adadin shekarun da mahaifiyar sa ta ce ya ke da su, to yawan shekarun sa kenan.
“Duk wanda ya ƙara tambayar ku adadin shekarun Tinubu,ku ce masa ya je lahira ya tambayo mahaifiyar sa,” inji Gbajabiamila.
A kan maganar zurfin ilmi kuwa, Gbajabiamila cewa ya yi, “kakaf a cikin masu takarar shugaban ƙasa babu wanda ya kai zurfin ilmin Tinubu. Ko haɗa ilmin su aka yi wuri ɗaya, bai kai gejin ilmin Tinubu ba.”
Gbajabiamila bai tsaya a nan ba, da ya koma kan zargin cin rashawa da wawurar kuɗaɗe kuwa, Gbajabiamila cewa ya yi, “a cikin manyan ƙasar nan babu wanda aka fi yi wa binciken ƙwaƙwaf kamar Tinubu, kuma har yau ba a same shi da laifin komai ba.
“Idan ‘yan adawa na damun ku kan takarar tikitin Muslim-Muslim, to ku ce masu waɗannan ‘yan takara zaɓin Allah ne, ba zaɓin mutum ba.”
Daga cikin waɗanda su ka halarci gangamin har da Gwamnan Legas Sanwo-Olu, Gwamna Nasiru El-Rufai na Kaduna, Shugaban APC Abdullahi Adamu, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Tinubu, Kashim Shettima da sauran wasu da dama.