Babbar Daraktar Ofishin Lura da Basussuka (DMO), Patience Oniha, ta bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan dalilan da su ka kasa hana Najeriya ƙarin ciwo bashi, shi ne saboda ba ta iya haƙo ɗanyen mai na adadin ganga miliyan 1.8 a kullum, wanda shi ne gejin da OPEC ta amince.
Da ta ke jawabi gaban Kwamitin Majalisar Dokokin Tarayya mai lura da Tallafi, Basussuka, Oniha ta ce da a ce a yanzu Najeriya za ta riƙa haƙo adadin gangar ɗanyen man da OPEC ta amince kowace ƙasa ta riƙa haƙowa, to Najeriya za ta iya daina yawan ciwo bashi.
Oniha ta ce yanzu farashin kowace gangar ɗanyen mai ya nunka daga farashin sa da aka yi kasafin kuɗin 2023.
A ƙididdigar watan Yuni, 2022 adadin kuɗin da ake bin Najeriya ya kai dala biliyan 103.3.
Yayin da ta yi kiran cewa a tashi a maida hankali wajen inganta hanyoyin bunƙasa fetur da kuma sauran hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga ƙasa.
Yayin zaman dai sai da Shugaban Kwamitin na Kuɗaɗen Tallafi da Basussuka, Ahmed Safana ya nemi jin dalilin yadda a cikin shekara ɗaya bashin da ake bin Najeriya ya ƙaru da naira tiriliyan 1.
Ko kwanan nan sai da Najeriya ta bayyana cewa an kwangila na bin Gwamnati bashin naira biliyan 785 na kuɗaɗen da su ka gina titina da gadoji.
Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana cewa a zaman yanzu haka ‘yan kwangilar da su ka gina titina da gadoji na bin Gwamnatin Najeriya bashin Naira biliyan 765.1.
Ya ce an yi ayyukan ne a manyan titinan gwamnatin tarayya da manyan gadojin da ke kan waɗannan titina.
Ya ce an bayar da naira biliyan 110.5 wajen ayyukan manyan titina domin fara biyan wannan ɗimbin bashi da ya bibiyi Gwamantin Tarayya a cikin kasafin 2022.
Fashola ya bayyana haka ne a ranar Talata, lokacin da ya ke kare kasafin 2023 a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai ta Ƙasa mai kula da Ayyuka.
“Ya zuwa watan Oktoba, 2022, Ma’aikatar Ayyuka na da bashin kuɗaɗen ‘yan kwangila da ba ta biya ba, har na naira 765, 017, 139,752.92, na ayyukan da ake kan yi na cikin kasafin 2022.”
A kan haka sai Fashola ya koka da yadda Najeriya ke kasa ɗaukar nauyin gudanar da ayyuka ba tare da ciwo bashi ba, haka kuma ya yi ƙorafi dangane da yadda ba a danƙara wa Ma’aikatar Ayyuka maƙudan kuɗaɗe a kasafin kuɗi.
Ya ce, “ana yi wa ɓangaren ayyuka ƙwauron kuɗi, ta yadda ta kai ana yin kasafin naira miliyan 200 ga ayyukan titunan da za su iya lashe naira biliyan 20 ko sama da haka.”
A kasafin 2022 an ware wa Ma’aikata da Gidaje Naira biliyan 515.9.
Fashola ya ce maganar gaskiya ma’aikatar sa na buƙatar naira tiriliyan 1.2 domin aiwatar da manyan ayyukan gina manyan titina, amma abin da aka ware mata a kasafin 2023, bai wuce Naira biliyan 198.9 ba.
Sai dai kuma ya ce hakan bai hana ma’aikatar sa kammala manyan ayyuka a kan manyan tituna 20 a cikin 2022 ba.
Discussion about this post