Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, David Babachir ya bayyana wasu dalilai da ya sa Kiristocin Arewa Kaf ɗin su za su zaɓi Peter Obi ne ba Tinubu ko Atiku ba a zaɓen 2023.
Cikin dalilan da Babachir ya bayar sun hada da zargin wai jam’iyyar APC ta tsaida Tinubu/Atiku waɗanda dukkan su musulmai ne don su muzguna wa kiristocin Najeriya. A cewar sa Babachir ya kara da wai idan har aka bari Tinubu da Shettima suka yi nasara to lallai Kiristocin Arewa sun Kaɗe.
” Sannan kuma da ake cewa wai muna goyon bayan Atiku Abubakar na PDP, karya ne, domin bamu bashi. Abinda yayi APC a wannan zaɓe shi yayi PDP, duk kanwar ja ce. Mu kiristocin Arewa ba za mu yi su ba, Obi zamu yi
Babachir ya kara da cewa ” Za su mara wa Obi baya kuma mu yi mishi aiki domin shine sabon jini, duk sauran dake takara a sauran jam’iyyun saura ne kawai, amma shine da mataimakinsa sabon jini ne masu karfi a jika.
” Sannan kuma, tuni muka gano cewa musamman jam’iyyar APC da ta tsaida Tinubu da Shettima, sun yi haka ne don su nuna kaskanci ga kiristocin Arewa, kuma idan aka bar su suka cimma burin su za su kawo rarrabuwan kai da rashin zaman lafiya a yankin duk da ko dama abin sai a hankali.
” Idan muka yi dubi ta ɓangaren Kashim Shettima, ya yi gwamna shekara 8 a jihar Barno, bai tsinana wa kiristoci komai ba, hasali ma a ƙarƙashin sa ne aka sace Ƴan matan Chibok, da Dapchi, aka kona Coci-coci da dama a jihar. Me zai iya yi in ba kara ruruta kiyayya da gaba a tsakanin mutane ba musamma kiristoci.
Idan ba a manta ba shi dai Babachir da ke wannan korafi an fatattake shi ne daga kujerar sakataren gwamnatin tarayya bayan samun sa da aka yi da hannu dumu dumu a badaƙalar wafce miliyoyin naira a harkallar kwangilar cire ciyawa a kogin Yobe.
Shugaba Buhari ya musanya shi da Boss Mustapha.
Discussion about this post