Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin fara haƙo ɗanyen mai a Kolmani, yankin da ke jihohin Bauchi da Gombe.
Wannan wani tarihi ne mai tabbatar da samun ɗanyen mai a Arewa, bayan shafe shekaru ana ta fafutikar aikin nema.
Cikin watan Oktoba, 2019 ne NNPL ta tabbatar da cewa an gano akwai ɗanyen mai da gas a ƙarƙashin ƙasar yankin Kolmani, kuma mai tarin yawan gaske.
Wurin wanda ke da faɗin gaske, ya shafi yankin Upper Benue Basin har zuwa Gongola Basin.
Kamfanin Sterling Global Oil, NNDC da NNPCL ne za su yi aikin haƙo ɗanyen man a Yankin Kolmani Oil and Gas Field.
Da ya ke ƙaddamar da fara haƙar ɗanyen man a Bauchi, Buhari ya ce aƙalla akwai ɗanyen mai a yankin fiye da ganga biliyan 1, kuma akwai gas zai kai cubic biliyan 500.
An dai daɗe ana gaganiyar neman ɗanyen man har zuwa cikin Oktoba, 2019 lokacin da aka tabbatar da samun sa.
Buhari ya ce samun ɗanyen man zai bunƙasa tattalin arziki, samar da aiki, samar da kuɗaɗen shiga da kuma inganta rayuwar mutanen yankin.
Ya ce ya zauna da Gwamnonin Gombe da Bauchi ya umarce su da su sa ido sosai, saboda aikin haƙar ɗanyen mai ɗin ya shafi mazauna yankin.
Discussion about this post