Nayi matukar mamaki dana ga rahoton da wata hukuma ta fitar “Wai jigawa ce jiha ta ukku a jerin gwannon jihohi talakawa” wannan rahoton dariya ma ya bani.
MU KALLI JIGAWA A KASUWANCI
Hakika akwai manyan kasuwanni na kasa da kasa har guda uku a jigawa sune “Maigatari, Gujungu, Sara” wannan kadai idan gwamnati ta zuba hannayen jari tare da gyarawa da bawa mutane jari domin Inganta sana’o’insu tabbas za’a samu arziki da kuma ayyukan yi.
A Maigatari ana kawo kayan masarufi da suka hadar da Gero, Dawa, Alkama, Shinkafa, Masara da sauran su. A fannin Kiwo kuma ga Shanu, Raguna, Tumakai, Awakai, Rakuma da sauran su, wani bincike ya nuna cewar kasuwar na daya daga cikin kasuwa mafi girma a Arewa da ake siyar da dabbobi yaya kake tunani idan gwamnati ta inganta harkokin KASUWANCI da gyara kasuwar?
Wannan fa duka hakama sauran kasuwannin suke, akwai sauran kasuwanni kanana da manya a jihar irin su shuwarin, kazaure, hadejia, gumel, ringim da sauran su.
MU KALLI JIGAWA A NOMA
Abun alfahari ne matuka irin yadda muke da kasar noma iya ganin da zalamar manoma a fadin jigawa ga ruwa na kogi a Hadejia, Ringim, Kazaure, kafin hausa, Auyo, Guri, da sauran su. Ana noma rani da damuna kuma noman irinsu shinkafa, kayan Miya, Masara, dawa, gero da sauran su.
Kana tunanin idan mutane zasu samu taki da sauran kayan noma hade da tallafin kudi, jigawa bazata zama abun kwatance a Africa ba?
MU KALLI JIGAWA A ILIMI
Muna da jami’a har guda uku, Dutse, Kafin hausa, Taura yanzu ga sabuwa a Babaura da hadejia da Birnin kudu, ga Poly har 4 ga makaruntun lafiya sama da 15 ga kwalejin ilimi a gumel da Kazaure.
Makarantar kwamfuta ta farko a Arewa a kazaure take, a baya sai da tafi kowacce a Africa amma yau ta durkeshe saboda rashin sanin ciwon kai.
Muna da masu degree sama da karamin lissafi ga masu NCE ga diploma idan an basu aiki, wasu jarin noma da kasuwa kenan anyi asara? Me ake da kudin rabano da kudin gwamnatin nigeria? Gine gine marasa amfani? Gina makaranta ba malamai? Asibitoci ba jami’ai? Ko me?
Allah kadai yasan albarkar dake cikin duwatsun mu dake cike da jigawa, amma rashin shugabanci yasa wai jigawa ce ta uku a talauci.
A dai sake tunani, dagaske jigawa tarin Allah ce. Allah bamu shugabanni adalai, masu tinanin gobe Amin.
Adamu Saleh maidalibai Kazaure.
salehadamu90@gmail.com
Discussion about this post