Kwana biyu bayan Babbar Kotun Tarayya ta tsige ɗan takarar APC na zabeni gwamna a Jihar Akwa Ibom, a ranar Litinin kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja ta tsige tsohon Minista Godswill Akpabio daga takarar sanatan Akwa Ibom ta Yamma.
A zaman kotun da aka yi ranar Litinin a Abuja, an
Maye gurbin da aka cire Akpabio da tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Udom Ekpoudom.
Kotun dai ta jingine hukuncin farko wanda Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yi, wadda ta ce Akpabio ne ya yi nasara a zaɓen fidda gwani, ba Ekpoudom ba.
“Za a iya tunawa cewa a ranar 27 Ga Mayu, 2022 an yi zaɓen fidda gwani na Sanatan Akwa Ibom ta Yamma, kuma kotu ta gamsu da cewa Udom Ekpoudom ne halastaccen ɗan takarar da ya yi nasara,” inji Kotun Ɗaukaka Ƙara.
Mai Shari’a Ɗanlami Senchi ne ya karanta hukuncin kotun, a madadin shi da sauran alƙalai biyun da su ka haɗu su uku su ka yanke hukuncin korar Akpabio daga takara.
Shi dai Akpabio ya tafi bilumbituwar takarar shugaban ƙasa, inda sai daga baya ne ya je ya yi wani zaɓen fidda gwani daban na ɓangaren magoya bayan sa, ba na uwar jam’iyya ba.
Kada a manta, ko a zaɓen gwamnan jihar Akwa Ibom, Akpabio ne ya janyo kotu ta hana APC shiga takarar zaɓen gwamna a jihar.
Ga shi kuma yanzu har yau a 2023, Babbar Kotun Tarayya da ke Uyo, ta yi fatali da ɗan takarar zaɓen gwamnan Jihar Akwa Ibom na jam’iyyar APC.
Mai Shari’a ya ce Akanimo Udofia bai cancanci tsayawa takarar gwamna a APC ba, saboda bai cika sharuɗɗan tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin APC ba.
A kan haka kotun ta ce a gaggauta sake sabon zaɓen fidda gwani cikin kwanaki 15, amma kada Udofia ya shiga zaɓen.
Tun farko dai tsohon Sanata Ita Enang ne ya garzaya kotu, ya kai ƙarar cewa wanda aka ce shi ya lashe zaɓen fidda gwanin ‘yan takarar gwamna a APC, bai cika kwanaki 30 da INEC ta ƙayyade ba kafin ya shiga takara.
Mai Shari’a ya yi bincike tare da amfani da hujjojin masu ƙara, cewa Udofia ya fita daga PDP ya koma APC bayan har ya rigaya ya sayi tikitin takarar gwamna a PDP.
Sannan kuma bai cika kwanaki 30 a PDP ba, majiyoyi da dama su ka ce dama tsohon Gwamnan Akwa Ibom ne, Godswill Akpabio ya jajibo shi, ya yi babakeren da ya tabbatar shi ya ci zaɓen fidda-gwanin, wanda kotu ta soke a ranar Litinin.
Discussion about this post