Sakataren hulda da Jama’a na jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Yusuf Idris ya bayyana cewa ba a taba samun shugaba irin shugaba Muhammadu Buhari a tarihin Najeriya ba.
A lokacin da ya ke tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya, Idris ya yi karin haske cewa Buhari ne shugaban da ya jagoranci Kasar nan da ba a taba samu ba.
” Abinda ya sa mutanen Najeriya ke yi wa gwamnatin Buhari mummunar fahimta shine na rashin tallata ayyuka da nasarorin da gwamnatin ta samu wanda shine ya kamaci mutane musamman makarraban sa su rika yi.
” Cikin irin ayyukan taimaka wa talakawa da gwamnatin Buhari ta bijiro su da suka hada da N-Power, Conditional Cash. Transfer, TraderMoni, Senior Citizens’ programe, wanda duka duk an kirkiro su don tallafawa talakawan Najeriya.
” Kamar mu a jihar Zamfara, sama da mutum 200,000 sun amafana da ire-iren wadannan tallafi da gwamnati ke badawa. Sannan kuma irin haka duk ana yin su a sauran jihohin kasarnan talakawa na amfana da su.
Discussion about this post