Shuagaban Hukumar Jiragen Kasan Najeriya, Fidet Okhiria ya karyata labaran da aka yada cewa wai jirgin Kasa na fasinjoji na Abuja-Kaduna zai dawo aiki gadan-gadan daga ranar 24 ga wannan wata.
Okhiria ya bayyana cewa akwai shirin dawo da aikin jirgin kasan amma ba a sanar da wata rana da zai fara aiki ba.
” Tabbas kamar yadda ministan Sufuri ya bayyana cewa jirgin zai fara aiki a cikin wannan wata, ba a sanar da wata rana da zai fara jigilar fasinjoji ba har yanzu, saboda haka mutane su yi watsi da wata rani da ake yadawa wai ranar ce zai fara aiki.
A karshe ya yi kira ga mutane da su yi watsi da wannan sanarwa cewa ba daga hukumar ta fito ba.
Discussion about this post