Ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin PDP, Atiku Abubakar ya yi wa Gombawa alƙawarin farfaɗo da Daɗin Kowa Dam domin ya riƙa samar da wutar lantarki ga ƙasa, idan har aka zaɓe shi a zaɓen 2023.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar dai ya yi wannan alƙawari ne lokacin da Rundunar Yaƙin PDP ta dira Gombe domin ci gaba da kamfen ɗin sa. Kuma ya yi alƙawarin gina dukkan titinan da su ka haɗe Jihar Gombe da Adamawa da Barno, Yobe da Bauchi.
Atiku ya ce ya tabbatar idan aka gina titinan waɗanda sun daɗe da lalacewa, harkokin kasuwanci da cinikayya a tsakanin jihohin biyar.
“Mu na kuma ƙara jaddada cewa dama Daɗin Kowa Dam wanda dama tun asali PDP ce ta gina shi domin samar da wuta da noman rani, to idan mu ka ci zaɓe za mu sake farfaɗo da shi domin bunƙasa lantarki da noman rani.
“Kuma za mu tabbatar cewa mun gina dukkan titinan da su ka haɗa tsakanin Gombe, Barno, Bauchi, Yobe da Adamawa, domin inganta harkokin cinikayya,” inji Atiku.
Atiku wanda ɗan asalin Jihar Adamawa ne, ya kwatanta kan sa da Firai Minista Abubakar Tafawa.
“Da yawa daga cikin ku ba a haife ki lokacin mulkin Abubakar Tafawa Ɓalewa ba. To a yau ga dama ta same ku ta sake samun wani Tafawa ɗin idan ku ka zaɓe ni.”
Shugaban Kamfen ɗin Shugaba Ƙasa na PDP, kuma Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya ce idan PDP ta yi nasara a 2023, tattalin arzikin ƙasa zai bunƙasa, darajar naira ita ma za ta farfaɗo.
Discussion about this post