Duk duniya dai ba za a taba yin tunanin cewa kasar Saudi Arabiya za ta iya cin koda kwallo ɗaya ne a wasa tsakanin ta da Argentina ba musamman a irin ƴan wasan da Argentina ta ke dasu.
Sai dai kuma abin ba a nan take ba domin kuwa a wasan Argentina ta farko wanda ta kara da Kasar Saudi Arabia ce, Saudiya ta lallasa ta da ci 2-1.
Abin da ya ba ɗan kallo mamaki shine ganin Argentina ce ta fara zura kwallo a ragar Saudiya ta hanyar bugun daga kai sai gola.
Messi ya jefa kwallon.
Hakan bai ta da wa Saudiya hankali ba, domin ba da dadewa ba bayan dawo daga hutun rabin lokaci suka farke wannan kwallo. Haka kuma da tafiya ta yi tafiya suka kara wa Argentina kwallo ta biyu.
Haka dai aka yi ta fafatawa kamar za a kamar ba za a ba, har lokaci ya ci duk da ko an kara mintina sama da 11 saboda dakatar da wasan da aka rika yi akai akai.
Wasan dai bai yi wa Argentina daɗi ba saboda ba haka suka ɗauka zata kasance ba.
Ga dukkan alamu dai Argentina ta raina kasar Saudiya ne tun farko sai gashi wankin hula ya kaita dare. Yan babbar kalubale a gabanta domin dole ta ci wasanta na biyu da na karshe idan tana so ta kai zagaye na gaba.
Discussion about this post