Babbar Kotun Tarayya da ke Uyo, ta yi fatali da ɗan takarar zaɓen gwamnan Jihar Akwa Ibom na jam’iyyar APC.
Mai Shari’a ya ce Akanimo Udofia bai cancanci tsayawa takarar gwamna a APC ba, saboda bai cika sharuɗɗan tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin APC ba.
A kan haka kotun ta ce a gaggauta sake sabon zaɓen fidda gwani cikin kwanaki 15, amma kada Udofia ya shiga zaɓen.
Tun farko dai tsohon Sanata Ita Enang ne ya garzaya kotu, ya kai ƙarar cewa wanda aka ce shi ya lashe zaɓen fidda gwanin ‘yan takarar gwamna a APC, bai cika kwanaki 30 da INEC ta ƙayyade ba kafin ya shiga takara.
Mai Shari’a ya yi bincike tare da amfani da hujjojin masu ƙara, cewa Udofia ya fita daga PDP ya koma APC bayan har ya rigaya ya sayi tikitin takarar gwamna a PDP.
Sannan kuma bai cika kwanaki 30 a PDP ba, majiyoyi da dama su ka ce dama tsohon Gwamnan Akwa Ibom ne, Godswill Akpabio ya jajibo shi, ya yi babakeren da ya tabbatar shi ya ci zaɓen fidda-gwanin, wanda kotu ta soke a ranar Litinin.