Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fara horas da malamai 3,700 domin dawo da koyar da darussan tarihi a makarantu
Ministan Harkokin Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana haka a taron da Ƙaramin Ministan Ilimi Goodluck Opiah ya wakilce shi, a Abuja.
An tattaro malamai 3,700 ta hanyar ɗauko malami 100 daga kowace jiha da kuma FCT Abuja.
Cikin 2009 da 2020 Gwamnatin Tarayya ta soke koyar da darussan tarihi a makarantu kwata-kwata.
Amma a 2016 zuwa 2018, Ministan Ilmi Adamu Adamu ya yi sanarwar za a dawo da koyar da darussan tarihi a makarantun firamare da Ƙananan Sakandare.
Hukumar UBEC ce aka ɗora wa nauyin horas da malaman a ƙarƙashin Hukumar Faɗaɗa Bincijmken Ilmi (NERDC).
Dama dai tun lokacin da gwamnatin Jonathan ta watsar da koyon darussan tarihi a sakandare, jama’a da dama sun yi ta ƙorafin cewa hakan zai lalata ƙwaƙwalen yara su kasa sanin tarihin shekaranjiya da jiya. Kuma yaro zai tashi a matsayin kifin rijiya, wanda bai san ko’ina ba.
Discussion about this post