Yanzu haka dai ƙudirin neman kafa hukumar kula da almajirai da yaran da ba su zuwa makaranta, ya samu zaman sauraren amincewa har zama biyu a Majalisar Wakilai ta Ƙasa.
Ƙudirin dai Ɗan Majalisar Tarayya Shehu Kakale ne ya bijiro da shi, wanda ɗan PDP ne a Jihar Sokoto shi da wasu mambobi 18.
Yanzu dai ya tsallake siraɗi na biyu. Da ya ke yamutsa gashin baki a kan ƙudirin, Kakale ya bayyana cewa su na so a kafa Hukumar Kula da Ilmintar da Almajirai da Yaran da ba su zuwa Makaranta, ta yadda za a zamanantar tsarin karatun na su. Hakan inji Kakale zai daƙile matsalar yawaitar yara marasa ilmi.
Kakale ya ce yawan yaran da ke gararamba ba su zuwa makaranta a ƙasar nan na buƙatar magancewa cikin gaggawa.
Ya ce hukumar za ta kuma riƙa horar da yaran koyon sana’o’i, ta yadda shirin zai rage fatara da talauci da kuma magance rashin aikin yi.
Kakale ya ce idan almajiran su ka samu ilmi mai inganci, zai iya kare su daga afkawa hannun ɓatagarin da za su iya gurɓata rayuwar su.”
Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Femi Gbajabiamila ya goyi bayan ƙudirin, kuma ya ce ya na da muhimmanci ƙwarai.
Shi ma Nicolas Ossai, ɗan PDP daga Delta, ya ce ƙudirin ba sabon abu ba ne, domin PDP ta yi wannan ƙoƙarin a shekarun baya.
Discussion about this post