Kwamishinan ilimin Jihar Bauchi, Aliyu Tilde, ya bayyana cewa uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ba ta nuna dattaku ba a irin hukuncin da ta yi wa Aminu Mohammed, matashin da yayi rubutu a kan ta ya saka a yanar gizo.
Tilde ya ce ” Gaskiya ban ji dadin da Hajiya Aisha Buhari ta ki sauraren rokon da ire-irena, da iyayen Aminu, da kungiyar dalibai, da jama’a da yawa suka mata ba kan cewa ta yafe wa yaron nan bayan ladabta shi da aka yi. BBC sun ce yau za a kai shi kotu.
” Ai al’umma gaba daya ta roke ka ma arziki ne. Amma ka yi mirsisi ka ki ji kuma ba halin dattaku ba ne.
” Ita kalmar “dattaku” da “dattijo” duk na Fulatanci ne. A Hausa muna ce masa halin girma. Halin girma a nan shi ne ka bar wa na kasa da kai kasonka, ko hakkinka ko ka yafe masa, ko ka girmama mutane ta hanyar karbar shawararsu, dss.
” A nan, abar kaunata ta kashe min gwiwa . Allah ya taimaka. Sad.
Don Allah jama’a banda zagi.
A baya, Tilde ya bayyana rashin jin dadin sa game da abinda wannan matashi ya yi yana mai cewa bai kyauta wa Aisha Buhari ba.
” Gaskiya wannan ba da’a ba ne kwata kwata. Kuma duk uba zai yi wa dansa fada idan ya ga ya rubuta wannan. Aibata mutum da halittarsa kuma ka kara da kazafi bai dace a ce tarbiyyar da yaranmu za su dauka ba ne. Na tabbata Malam Adamu Mohammed, mahaifin Aminu, bai taba yi wa wani shugabansa haka ba. Amma ga d’ansa ya yi. A ina wannan d’an namu, yana dalibi, ya tsinci wannan gubar har ya sha ta kai masa karo?
Discussion about this post