Ƴan sandan jihar Akwa Ibom sun bayyana cewa sun damƙe wani magidanci wanda ya kashe ƴar sa a dalilin rashin jituwa da ta shiga tsakanin su.
Mahaifin Sunday Etukudo ya kashe ƴar sa ne a lokacin da suka kaure da faɗa, sai ƴar Etukudu ta damke wa mahaifin ‘ƴaƴqn marainai.
Daga nan ne fa sai ya wawuri faskare ya sheme ta da shi. Bayan ta faɗi ta gama shureshurenta ta mutu sai, ya suntume ta ya haka rami a cikin gidan sa ya binne ta.
Kakakin rundunar ƴan sandan SP Odiko Macdon,ya ce bayan an gudanar da bincike sai aka gano cewa da ya kashe ƴar ta sa mai suna Ofonmbuk Ime Sunday, ya binne ta a gidan shi.
Kamar yadda Daily Nigerian ta buga a shafinta binciken ƴan sandan ya kai ga har sai da aka haƙo ta daga kasa aka ci gaba da bincike.
Discussion about this post