Ƴan bindiga sun yi awon gaba da mutum 44 a kauyen Kanwa dake karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara ranar Alhamis.
Daga cikin mutanen da maharan suka tafi da su akwai mata da yara kanana 39 da maza biyar
Wata majiya daga kauyen ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa mata biyar daga cikin waɗandada maharan suka tafi da su sun arce daga hannun maharan sun dawo gida.
Wani mazaunin Zurmi Musa Abdullahi ya bayyana wa Jaridar nan cewa ‘yan bindigan sun shigo kauyen a cikin daren Alhamis.
“Suna shigowa kauyen sai suka fara tara mutane. Maza kan gudu su boye cikin daji saboda ‘yan bindiga na kashe maza sai dai a wannan rana maza biyar ba su arce ba a lokacin da ƴan bindigan suka kawo harin.
Ya ce ana zargin cewa yaran gogarma Dankarami ne suka sace mutanen kuma har yanzu ‘yan bindigan ba su kira kowa ba tukunna.
Wani da baya so a fadi sunnan sa saboda tsaro ya tabbatar cewa mata biyar daga cikin waɗanda aka sace sun arce kuma sun dawo gida.
“Tabas mata biyar sun dawo gida tare da taimakon ‘yan banga. Matan sun ce sun tsere daga hannun maharan saboda yawan mutanen dake tsare a wurin maharan.
Harajin Naira miliyan 20
‘Yan bindigan dake yankin Shinkafi, Moriki zuwa ƙauyen Isa sun sakawa kauyen Moriki harajin Naira miliyan 20.
Moriki na daga cikin kauyukan da suka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga a karamar hukumar Zurmi.
Wani mazaunin kauyen Jamilu Shehu ya ce zuwa yanzu mutane sun fara tara kudaden harajin da za a biya maharan.
Shehu ya ce wasu dattawa daga kauyen bayyan sun tattauna da maharan dake karkashin Turji sun amince lallai za a biya wannan kuɗi.
Discussion about this post