Sanata Ifeanyi Ararume ya maka Shugaba Muhammadu Buhari kotu, saboda shugaban ƙasa ya janye takardar shaidar naɗa shi shugaban NNPCL marar cikakken iko da Buhari ɗin ya yi.
An dai naɗa Ararume cikin Satumba 2021, amma sai ana cire sunan sa tun kafin a rantsar da mambonin hukumar gudanarwar NNPCL ɗin a cikin January, 2022.
Jin haushin haka sai Ararume wanda Sanata ne a jihar Imo, ya garzaya Babbar Kotun Tarayya ta Imo a ranar 12 Ga Satumba, 2022 ya maka Buhari kotu, inda ya ƙalubalanci cirewar da aka yi masa watanni takwas baya.
Ya shaida wa kotu ce an cire shi ba bisa ƙa’idar da ya kamata a cire shi ba. Ya ce an janyo masa rikicewar ayyukan ofishin sa.
Ararume ya ce cire shi an karya Doka Kamfanoni ta CAMA 2021 da kuma dokar Harkokin Fetur (PIA) ta 2021.
Ya roƙi kotu cewa sai a biya shi diyyar Naira biliyan 100, sannan kuma kotu ta bayar da umarnin cewa a maida kan muƙamin sa da aka naɗa shi da farko na Shugaban Kwamitin Hukumar NNPCL wanda aka cire shi tun kafin ya shiga ofis.
Sannan kuma ya roƙi kotu ta soke du wani aiki ko wani umarni da Hukumar NNPCL ta yi tun daga ranar da aka naɗa mata shugabannin hukumar gudanarwa zuwa yau.
An dai naɗa shi cikin Satumba 2021.
Discussion about this post