Kamar yadda a ka yi danbarwa a kujerar Sanatan Yobe ta Arewa tsakanin Shugaban Majalissar Dokoki da kuma Hon. Machina, da Jama’iyar APC, wanda da ga baya gaskiya ta tabbata, duk da karfin da a ka ga Ahmed Lawan na da shi.
Irin wannan danbarwa ce take faruwa a kujerar Majalissar Wakilai ta Hadejia/ Auyo/Kafin-Hausa a jama’iyar PDP tsakanin Mohammed Jarma da Isah Dansidi.
Bayan an gudanar da zaben fidda gwani a garin Hadejia a gaban masu ruwa da tsaki a harkar zaben, hadda masu sanya ido ranar 22 ga watan Mayu, 2922, wanda shi Mohammed Jarma ya lashe.
Sakamakon zaben ya nuna cewa, Mohammed Jarma ya sami kuri’a 55 yayin da abokin karawar sa Isah Dansidi ya sami kuri’u 44.
Wakilan zaben a gaban kowa suka tabbatar da Mohammed Jarma a matsayin wanda ya lashe zaben a gaban kowa da kowa.
Abin mamaki sai gashi da ga baya kwatsam uwar jama’iyar PDP ta bada sunan Isah Dansidi a matsayin wanda zai yi wa PDP takara a kujerar wakilcin Hadejia/Auyo/Kafin-Hausa. Bayan shine yazo na biyu a zaben fidda gwanin da a kayi.
Wannan ya nuna cewa zaben da wakilan Jama’iyar PDP wato delegates suka yi da alama bai yiwa kartikan jama’iyar dadi ba, shi yasa ta ko yaya sai sun chanja wannan da takara da ya lashe wannan zaben fidda gwani.
Amma fa ga duk wanda yasan yadda dokar zabe take a wannan kaka, ya san yin hakan kamar da wuya.
Dama Hadejia/Auyo/Kafin-Hausa na fama da rashin inganchin wakilci a wannan majalissa, a shekarun nan da a ka yi da dawowar mulkin dimokaradiyya, babu wani kudiri da wakilin su daya yayi a zaman sa na majalissa, haka abin yake a wannan majalissar ma ta tara.
Dama ba yadda za a yi a samu wakilci mai inganci ba tare da gudunmawar jama’iyar siyasa ba, amma shugabannin jama’iyun nan da kartukan siyasa ke hama ruwa gudu, kamar yadda muke gani a yanzu.
Duk da cewa a kwai zaton samun cigaba a yanci na dimokaradiya, wannan karon za a samu chanji, bayan bin ka’idodi na Electrol Act wajen zaben fidda gwani.
Samun nasarar Bashir Machina a shari’ar sa da Ahmed Lawan da Jama’iyar APC, ya nuna karara cewa shari’a a yanzu tana aikin ta, a kwai zaton za a tabbatar wa da mutane hakkin su a kan abin da suka zaba.
Muna dakon sauraren sakamakon kotu a kan wannan batu, tunda batun na gaban alkali.
Fatan mu shine, samun adalchi don tabbatarwa wa mutane abin da suka zaba.
Ita dimokaradiyya ba komai bace, face bawa al’ummah damar zaben wakilan su da shugabannin su, ba tare da tunzurawa ba.
Yin karkarfa d chushe a cikin harkar mulki, ba komai zai kawo ba sai face yiwa dimokaradiyar sartse.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post