Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a kammala gadar ‘2nd Niger’ da ke jihar Anambra kafin Kirsimeti.
Kwantorolan ayyuka na jihar Anambra, Seyi Martins ya bayyana cewa aikin gadar yakai kashi 95 cikin 100 kuma matafiya za su yi amfani da gadar a lokacin Kirsimetin bana.
” Ba kamar yadda ake ta watsawa a kafafen yada labarai ba wai sai shekarar 2024 za a gama wannan gada, ina so in sanar muku cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin lallai a kammala wannan hanya a wannan shekara kuma yanzu saura karishe ne kawai. Matafiya za su yi amafani da gadar a lokacin kirsimeti.
Gadar 2nd Niger na daga cikin manyan alkawuran da gwamnatin Buhari ta dauka a lokacin kamfen din 2015. Zuwa yanzu aiki ya kai gaban goshi ana sa ran kafin kirsimeti za a gama aikin hanyar matafiya za su amfani da gadar.
Discussion about this post