Gwamnatin Tarayya ta yi wa sabbin ƙungiyoyin malaman jami’o’i biyu rajista, a yunƙurin gwamnatin na karya lagon ASUU.
Ƙungiyoyin biyu a aka bai wa katin shaidar rajista sun haɗa da NAMDA, wato Medical and Dental Academic da kuma CONUA, wato Congress of Nigerian University Academics.
Ministan Ƙwadago Chris Ngige ne ya damƙa wa shugabannin ƙungiyoyin satifiket a ofishin sa, a ranar Talata.
Ƙirƙiro sabbin ƙungiyoyin malaman jami’o’in biyu dai wani yunƙuri ne da gwamnati ta yi domin karya ASUU, ƙungiyar da mambobin ta ke yajin aiki tsawon watanni takwas kenan.
“Waɗannan ƙungiyoyin za su ci gaba da wanzuwa su na gudanar da harkokin su kafaɗa da kafaɗa da ASUU,” haka Ngige ya bayyana yayin da ya ke jawo wasu ayoyi daga cikin Kundin Dokar Aikin Ƙwadago ta Kungiyar Kare ‘Yancin Ma’aikata ta Ƙasa da Ƙasa (ILO), wato International Labour Organization, Sashe na 87 da na 98, wanda ya ce sassan biyu ne su ka bayar da ‘yancin kafa ƙungiya ga duk wani rukuni ko gungun da ke buƙatar yin haka.
Ngige ya shawarci sabbin ƙungiyoyin biyu kada su riƙa shiga sharo ba shanu cikin harkokin hukumar gudanarwar jami’o’in da su ke koyarwa a ciki.
Ya ce jajircewar da ASUU ta yi cewa tilas sai dai a riƙa biyan malaman jami’o’i albashi bisa tsarin UTAS, katsalandan ne ƙungiyar ta yi a cikin ‘yanci da haƙƙin da doka ta bai wa wanda ya ɗauki ma’aikaci aiki.
“Ai ya kamata kai da aka ɗauka aiki ka fara mutunta ‘yanci da haƙƙin wanda ya ɗauke ka aiki, kafin shi wanda ya ɗauke ka ɗin ya mutunta ‘yanci da haƙƙin ka.”
A taƙaice Ngige na ƙoƙarin nuna cewa bai yiwuwa gwamnati ta ɗauki mutum aiki, sannan kuma ya ce shi zai kafa mata dokar yadda ya ke so ya yi mata aikin.
“Kada ku malaman jami’o’i ku riƙa shiga harkokin hukumar gudanarwar jami’o’in ku. Misali, babu ruwan mu da shiga siyasar wanda zai zama shugaban hukumar gudanarwar jami’a ko Shugaban Jami’a (Vice-Chancellor).
Haka nan Ngige ya sanar da sabbin ƙungiyoyin cewa hukumar gudanarwar kowace jami’a ba za ta shiga cikin sha’anin zaɓen shugabannin sabbin ƙungiyoyin na malaman jami’a ba, kamar yadda kundin tsarin dokokin ƙungiyoyin ya gindaya.
Kafa Ƙungiyoyin sabbi guda biyu ya biyo bayan kika-kakar da ake ta fama tsawon watanni da dama tsakanin Minista Ngige da Shugaban ASUU, Emmanual Osodeke.
Su biyun dai sun yi cacar-baki mai zafi a ranar Alhamis, yayin da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya gayyaci su biyun taron sasanta matsalolin ASUU da Gwamnatin Tarayya.
Ngige ya zargi Osodeke da yi wa gwamnati ƙafar ungulu wajen ƙoƙarin ta na ganin an kawo ƙarshen rikici da ASUU.
Sannan kuma Ngige ya zargi Osodeke da ingiza ‘yan Najeriya su tsani Gwamnatin Buhari, ta hanyar nuna wa duniya cewa gwamnati ce ba ta cika alƙawurran da ta riƙa ɗauka a baya.
Yayin da CONUA ke da hedikwatar ta a Jami’ar Obafemi Awolowo University (OAU), ta fara ƙoƙarin rajista tun cikin 2018 bayan ta ɓalle daga ASUU.
Biyu Sunmonu wanda malami ne a OAU, shi ne sabon shugaban ta.
Ita kuma CONUA an kafa ta ne tun cikin 2018, inda yanzu haka ta yi ikirarin ta na da rassa 17 a cikin jami’o’in Najeriya daban-daban.
Shi kuma Osodeke ya ce Ngige bai naƙalci komai ba zai baza ƙarairayi kawai.
Discussion about this post