Shugaba Muhammadu Buhari ya hori Sojojin Najeriya su bazama a faɗin Najeriya su samar da irin gagarimar nasarar da su ka samar ko’ina irin wadda su ka samar a Arewa maso Gabas.
Buhari ya ce wannan gagarimar nasara da sojojin su ka samu, ta tabbata ne dalilin gwamnatin sa ta samar da manyan makamai da sauran kayan yaƙin da shekaru 38 a baya gwamnatocin baya ba su samar da irin su ba.
Buhari ya yaba wa gwamnatin sa da kan sa cewa a cikin shekaru bakwai, ya sayo makamai da sauran kayan yaƙin da shekaru 38 baya ba a sayo irin su ba.
Ya yi jinjinar yayin da ya ke jawabi a wurin bukin yaje Ƙananan Hafsoshi da kuma ƙaddamar da wasu sabbi na Sojojin Ruwa, Sojojin Ƙasa da na Sama, a NDA, Kaduna.
A wurin ne Buhari ya lissafa irin tulin kayan yaƙin da ya ce cikin shekaru bakwai gwamnatin sa ta samar.
Ya ce ba a taɓa samun gwamnatin da ta yi irin ƙoƙarin ta sa wajen sayo manyan makamai da kayan yaƙi ga sojoji ba, tun shekaru 38 da su ka gabata.
Buhari ya kuma jinjina wa Sojojin Najeriya dangane da yadda su ka ceto ragowar fasinjojin jirgin ƙasan nan su 23 da ke hannun ‘yan ta’adda, waɗanda su ka shafe watanni shida a daji tsare.
Buhari ya ce abin girmamawa ne a gare shi, ganin yadda ya halarci bikin yaye ƙananan hafsoshin na 69, wanda kuma shi ne na ƙarshe da zai halarta kafin cikar wa’adin mulkin sa.
“Lokacin da wannan gwamnati ta hau mulki cikin 2015, ta samu ƙasar nan komai na gwamnati a ragargaje. Ƙasa ba lafiya ta ko’ina bama-bamai ne ke tashi a ƙasar nan. Amma a haka mu ka tashi haiƙan sai da mu ka daƙile wannan matsalar.
“Wannan gwamnatin ta sayo wa Sojojin Ruwa jirage 550, waɗanda tuni har 319 sun iso Najeriya.
Kuma mun ƙara yawan jiragen yaƙi na Sojojin Sama da kashi 38 bisa 100, sannan kuma mu ka samar da kayan gyara tare da gyara kashi fiye da 70 cikin 100.
“Su kuma Sojojin Ƙasa an sayo masu motocin yaƙi fiye da 2000, an sayo bindigogi da sauran kayan yaƙi. Sannan kuma an ƙara wa dukkan bangarorin sojojin uku yawan kuɗaɗen da ake kashe masu a kowace shekara. Kamar yadda su ma sauran hukumomin tsaro sun ci irin wannan gajiyar.
Buhari ya jinjina wa Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Leo Irabor, wanda ya ce shi ya jagoranci ceto ragowar fasinjojin jirgin ƙasan nan su 23. Kuma ya gode wa sauran hukumomin tsaro.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Buhari ya jinjina wa gwamnatin sa bayan sojoji sun ceto ragowar fasinjojin jirgin ƙasa 23.
A ranar Laraba ce gwamnatin tarayya ta bada sanarwar cewa sojojin Najeriya sun kuɓutar da ragowar fasinjojin su 23, bayan sun shafe kwanaki 192 a hannun ‘yan ta’adda.
Sanarwar ta ce an samu nasarar kuɓutar da su ne misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Laraba.
Sai dai kuma har yanzu ba a san yadda aka kuɓutar da su ɗin ba, sannan kuma ba a bayyana shin an kashe ‘yan ta’addar ne ko salum-alum aka kuɓutar da su.
Ragowar fasinjojin dai sun samu kuɓuta bayan sun shafe fiye da watanni shida a hannun ‘yan bindiga.
Discussion about this post