Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa ƴan Najeriya cewa wannan shine jawabin sa na karshe a matsayin shugaban kasar Najeriya, kuma yana godewa ƴan Najeriya bisa damar da suka bashi a tsawon wannan lokaci ya dasa Najeriya kan turba tagari.
A cikin jawabin sa na ranar 1 ga watan Oktoba, Buhari ya ce karkashin mulkin sa an samu ci gaba ma su yawa da basu kirguwa saboda jajircewar gwamnatin da kuma maida hankali wajen ganin ƴan Najeriya sun amfana da arzikin da kasar ta ke da shi.
Sannan kuma ya yi kira ga malaman jami’o’in kasar nan su koma aiki dalibai su koma makaranta.
” Ina yin kira ga malaman jami’o’in kasar nan su koma aiki, dalibai su koma karatu. Ina tabbatar musu da cewa zamu yi duk abinda za mu iya yi don biya musu bukatun su daidai karfin gwamnati.
Ya kara da da cewa karkashin sa zai tabbatar an gudanar da zaɓuka cikin kwanciyar hankalin da gaskiya.
” Za mu tabbatar an gudanar da zaɓukan dake tafe cikin gaskiya da amana ba tare da an yi wa wani murɗiya ba. Hakan na daga cikin nasarorin da muka samu a zaɓukan da aka yi a jihohin Anambra, Osun da Ekiti wanda mutane suka zaɓi wanda suke so.
Discussion about this post