Mummunan halin ƙuncin da al’ummar Jihar Zamfara su ka shiga na kisa, fashi, garkuwa, fyaɗe da tarwatsa garuruwa bai sa wa Gwamna Bello Matawalle tausayin ƙyamar yin walle-walle da maƙudan kuɗaɗen al’ummar jihar ba.
A halin da ake ciki yanzu, Hukumar EFCC ta bankaɗo wasu kantama-kantaman gidaje guda shida da ta ce Bello Matawalle ya mallake su da kuɗaɗen sata, bayan ya zama gwamna.
EFCC ta ce Matawalle ya mallaki gidajen ne cikin 2020, lokacin har ya haura shekara ɗaya da zama gwamna.
Hakan ya na nufin dai kafin ya zama gwamna bai mallaki gidajen ba.
Ba a nan Binciken EFCC ya tsaya ba, hukumar ta kuma tabbatar wa Babbar Kotun Tarayya ta Abuja cewa an sayi gidajen guda shida da kuɗaɗen Gwamantin Jihar Zamfara, waɗanda ya kamata a yi wa al’ummar jihar ayyukan rage masu raɗaɗin ƙuncin rayuwa a hannun ‘yan bindiga.
Bayanin wannan gagarimar sata dai ya na a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya ta Abuja.
A ranar 14 Ga Oktoba ce Kotun Tarayya ɗin ta yana EFCC ƙwace gidajen guda 6 daga hannun Gwamna Matawalle.
Mai Shari’a Ekwo ya umarci EFCC cewa sai dai ta ci gaba da sa-ido kan gidajen, kuma ta adana hujjojin ta, har sai ranar da Gwamna Matawalle ya sauka daga mulki sannan ta damƙe shi, ta kai shi kotu, sannan a ƙwace gidajen.
Maka-makan Gidan Da Gwamna Matawalle Ya Saya Da Kuɗaɗen Talakawan Zamfara -EFCC:
1. Gida mai lamba 729, a unguwar hamshaƙai da ke Idu Layout, Abuja.
2. Gida mai lamba 1327, unguwar riƙaƙƙun attajirai, Cadastral Zone, Maitama, Abuja.
3. Gida mai lamba 2934, shi ma a Cadastral Zone, Maitama Abuja.
4. Gida mai lamba 730, shi ma a Cadastral Zone, Shiyar A06, Maitama, Abuja.
5. Gida mai lamba 2804, Shiyyar AO6, Cadastral Zone, Maitama, Abuja.
6. Gida mai lamba 515, B100, Kubwa.
EFCC ta ce Gwamna Matawalle ya karya Sashe na 17 (1)(2)(3).
Tsananin Rashin Tausayi: Yadda Aka Kama Gwamnan Zamfara Ya Na Jidar Biliyoyin Kuɗaɗen Jihar:
CIkin watan Oktoba, 2020 EFCC ta samu takardar ƙorafin yadda ake jidar kuɗaɗen Zamfara, ana sayen manyan kadarori da su a Abuja.
EFCC ta bi diddigin kuɗaɗen, ta gano cewa a karon farko an oamfaci naira biliyan biyu (N2, 117, 751, 000.00) an lafta cikin wani asusu mai lamba 1017028409 da ke Zenith Bank.
EFCC ta gano cewa asusun na Hukumar Zuba Jari da Bunƙasa Kasuwanci ne.
Daga nan sai wani gwanin iya karkatar da kuɗaɗe mai suna Abubakar Halliru ya tuntuɓi wani Sani Baƙo, ya ce za a kwaso kuɗaɗen daga asusun Zenith, a danƙara su cikin asusun kamfanin sa. Aka ce masa za a yi amfani da sunan kamfanin sa Aceworld Consult a sayi kadarori. Kuma hakan aka yi.
A kotu dai EFCC ta riƙa zato kwafen takardun hujjojin cewa Gwamna Matawalle ne ya sayi gidajen, ta na gabatarwa kotu.
Sai dai kuma kotu ta ce a yanzu Matawalle na sanye da sulken kariya, a matsayin sa na gwamna.
Saboda haka sai dai a bari har sai ya sauka, sannan a ƙwace gidajen, kuma a gurfanar da shi kotu.
Matawalle ya fice daga PDP ya koma APC bayan ya sayi maka-makan gidajen.
Discussion about this post