Tsohon Gwamnan Jihar Neja Babangida Aliyu, ya bayyana cewa a iyar yawan masu takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2023, Atiku Abubakar na PDP ya fi sauran ƙoshin lafiyar da zai yi shugabancin da za a ci moriyar sa.
Aliyu ya yi wannan furuci ne bayan fitar wani faifan bidiyon da aka nuno ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu a kan keken motsa jiki ya na cilla gudu amma a tsaye wuri ɗaya.
An nuno bidiyon ne yayin da jama’a ke cike da tambayoyin halin da Tinubu ke ciki, wanda ake cewa ya na Landan ya na jiyya. Har ta kai wasu ma na cewa Tinubu na tunanin janyewa saboda rashin ƙoshin lafiya.
“Na ga hoton wani mutum a jarida ya na zaune kan keken motsa jiki. To in dai ka na lafiya ƙalau, don me sai ka nemi an nuno ka a kan keken motsa jiki? Me ka ke so ka nuna wa mutane?
“Atiku Abubakar ya fi sauran ‘yan takara lafiya. Kuma shi ba ya ma buƙatar sai an nuna shi kan keken motsa jiki don ya tabbatar da lafiyar sa,” inji Aliyu, wanda ya yi gwamna a Neja daga 2007 zuwa 2015.
Aliyu ya ce Atiku ne kaɗai zai iya kawo ƙarshen Boko Haram, shi ne zai iya ƙwato duk wauraren da ke hannun ‘yan ta’adda. Kuma shi ne zai magance matsalar ‘yan bindiga.
Da ya koma kan tattalin arzikin ƙasa, Aliyu ya ce Atiku ne zai iya fitar da ‘yan Najeriya daga ƙuncin rayuwar da su ka shiga ƙarƙashin mulkin APC.
Haka nan barin ilmi wanda ya ce ɗaliban jami’a sun daɗe zaune a gida, yayin da makarantun sakandare sun kasance a lalace. Ya ce Atiku ne zai kawo ƙarshen wannan matsalar tare da hana sake afkuwar ta ko makamancin ta.
Ya ce irin matsalar tattalin arziki da ya shafi Najeriya, Atiku ne kaɗai zai magance ta.
“Gwamnatin APC yanzu haka ɗanyen man da ta ke haƙowa bai wuce ganga 600,000 a kullum ba. Sauran duk sace shi ake yi. Atiku ne zai iya kawo ƙarshen wannan gagarimar satar ɗanyen mai da ke yi a ƙarƙashin gwamnatin APC.”
Discussion about this post