Cibiyar yada labarai ta kasa da kasa (IPI) a Najeriya ta yi Allah-wadai da umarnin da gwamnatin jihar Zamfara ta bayar na rufe wasu gidajen yada labarai da ke aiki a jihar, inda ta bayyana matakin a matsayin kamakarya kuma ba za a amince da shi ba.
IPI Nigeria a cikin wata sanarwa da shugabanta Musikilu Mojeed ya fitar ta ce gwamnatin jihar Zamfara ba ta da hurumin rufe kafafen yada labarai, don haka ta yi kira ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara da kada ya aiwatar da dokar da gwamnati ta kafa ba bisa ka’ida ba.
“Rufe kafafen yaɗa labarai ya saba wa ƴancin faɗin albarkacin baki, wanda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bada wannan dama.
Idan ba a manta ba a dalilin watsa kamfen ɗin ɗan takaran gwamna na PDP, ya sa Matawalle ya rufe NTA da wasu gidajen watsa labarai.
” Shi fa Matawalle ba a yi masa katsalandan, idan ya ce ga abinda ya ke so, ka yi masa taurin kai to zai ko nuna maka shi Dodo ne. Da ma kuma haka ake masa kirari a Zamfara.
Wannan shine kalaman wani dafa cikin ɗan jam’iyyar APC kuma makusancin gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a lokacin da yake hira da wakilin mu.
Gwamna Matawalle ya ba da umarnin a rufe gidan talabijin na kasa NTA da wasu gidajen watsa labarai masu zaman kansu har biyar dake faɗin jihar saboda sun watsa kamfen din ɗan takaran gwamnan jihar na jam’iyyar PDP. Lawal Dauda.
Ko da yake taron ya cikaro da hatsaniyar gaske inda aka yi arangama tsakanin ƴan APC da na PDP a lokacin taron.
An ruwaito cewa ɗan takaran gwamnan jihar na PDP, Dauda ya samu tarba mai yawan gaske daga magoya bayan PDP a jihar da hakan ya fusata gwamna Matawalle da ƴan APC.
Gwamnatin jihar Zamfara ta saka dokar hana taron siyasa ko a gidan ka ne.
Gwamnati ta ce ta saka wannan doka ne saboda matsalar tsaro da ya ke neman dawo wa da zafin sa a jihar, kamar yadda Ibrahim Dosara ya sanar a wata takar da da gwamnati ta fitar a garin Gusau.
Dalilin haka ya sa gwamnati ta saka dokar dakatar da duk wani taron siyasa har da ita kanta jam’iyya mai mulki, wato APC.
Magoya bayan APC sun ce ƴan PDP sun kawo musu hari a lokacin kamfen ɗin su. An ruwaito cewa akalla mutum 14 ne aka ji wa rauni sannan mutum ɗaya ya rigamu gidan gaskiya.
Discussion about this post