Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, Bola Tinubu, ya tabbatar da cewa zai yi iyakar dukkan abin da ya wajaba domin ya kakkaɓe barazanar rashin tsaro, musamman ‘yan bindiga a ƙasar nan.
A janwabin sa wurin Taron Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa, a ranar Litinin a Kaduna, Tinubu ya ce “zan yi amfani da duk abin da gwamnati na ya wajaba ta yi amfani da shi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.
Taron wanda aka gudanar, Tinubu ya ce shi ba baƙon zuwa Arewa House ba ne, domin ko shekarar da ta gabata, shi ne Shugaban Lakcar Tunawa da Sardauna.
“Ni ba baƙo ba ne a wannan wuri, na sha zuwa lakca, domin ko shekarar da ta gabata ni ne Shugaban Lakcar Tunawa da Sardauna.
“Zuwa wurin nan ya na tuna mana manya ‘yan kishin ƙasa da kishin al’umma irin su Sa Ahmadu Bello Sardauna, wanda ya gina al’umma kuma ya gina cibiyoyin ilmi.”
Da ya ke magana kan matsalar tsaro musamman ‘yan bindiga, Tinubu ya ce zai yi irin abin da ya yi har ya wanzar da tsaro a jihar Legas, a lokacin da ya zama gwamna a 1999.
“Lokacin da na zama Gwamna cikin 1999, na samu Legas hannun ‘yan bindigar cikin birane, waɗanda su ka mamaye yawancin titina, sai yadda su ka ga dama su ke yi, wajen aikata munanan laifuka.
“Amma mun shigo da tsare-tsaren da mu ka kakkaɓe ɓatagari, har ta kai Legas ta zama son kowa, ƙin wanda ya rasa samu.
“Saboda haka za mu bi ƙasar nan mu samar da irin tsaron da muka samar wa Legas, ta yadda kowane wuri zai zama abin sha’awa mai cike da tsaro da zaman lafiya.”
Tinubu ya ce idan ya yi nasara, gwamnatin sa za ta rugurguje duk wasu masu neman hargitsa Najeriya.
Da ya taɓo tattalin arzikin ƙasa kuwa, Tinubu ya ce za a inganta tsarin zuba jari, maida hankali wajen bunƙasa noma, inganta tattalin arzikin fasahar zamani, kuma gwamnatin sa za ta mara wa masu masana’antu ta yadda za a bunƙasa su, sannan a farfaɗo da waɗanda su ka durƙushe.
Jagaban na Borgu ya ce gwamnatin sa za ta samar da aikin yi ga ‘yan Najeriya, za ta inganta wutar lantarki, albarkatun ƙarƙashin ƙasa, fannin ilmi, kuma za ta magance yawan gararambar da yara ke yi marasa samun galihun zuwa makaranta.
Discussion about this post