Wani gungun ‘yan bindigar da su ka yi garkuwa da ‘yan mata, ‘ya’yan toshon Akanta Janar na Jihar Zamfara, sun yi barazanar maida su riƙaƙƙun ‘yan ta’adda, matsawar ba a gaggauta biyan kuɗin fansar su ba.
Cikin wani bidiyo mai tsawon minti 2:39, an nuno ‘yan matan Zulaiha da Zainab su na sarrafa zabgegiyar bindigar nan ta harbo jirgin yaƙi, wato tashi-gari-barde, AK47 da LMG.
Bidiyon wanda aka yaɗa a ranar Litinin, a ranar dai yaran sun shafe kwanaki 128 a tsare cikin daji a hannun ‘yan bindiga.
An sace su ne tare da wasu ‘ya’ya da ‘yan uwan tsohon Akanta Janar ɗin mai suna Abubakar Bala-Farfaru, tun a cikin watan Yuni.
Daga baya an biya kuɗi aka saki wasu, amma a yanzu saura Zulaiha da Zainab da kuma wani hadimin gidan tsohon Akanta Janar ɗin.
A cikin bidiyon, wani ɗan bindiga ya riƙa yin barazanar cewa idan ba a biya kuɗin fansar su ba, to za su maida su ‘yan ta’adda, su riƙa fita kai hare-hare a gidajen masu kuɗi da makarantu tare da ‘yan matan.
Sun ce ba wasa ko ƙarya su ke yi ba. “Za mu riƙa sa su gaba su na nuna mana gidajen attajirai da makarantu mu na zuwa mu na kamo waɗanda za mu yi garkuwa da su.
Haka nan kuma a cikin bidiyon, an nuno Zulaiha ta na roƙon mahaifin su a cikin murya mai ban-tausayi, cewa ya gaggauta biyan kuɗi ya karɓo fansar su.
“Baba don Allah ka taimake mu, ka dubi halin da mu ke ciki. Ka biya kuɗi a sake mu. Kada ka bi ra’ayin masu cewa a daina biyan kuɗin fansa.”
Wakilin mu ya tura wa mahaifin yaran saƙon tes, amma bai maida amsa ba.
Sai dai wata majiyar da ke kusa da iyalan ta tabbatar wa wakilin mu cewa a baya Abubakar ya biya kuɗin da aka saki wasu da aka yi garkuwa da su tare da Zulaiha da Zainab.
“Amma a gaskiya yanzu ba shi da wasu kuɗin da zai ɗauka ya bayar a saki sauran ‘ya’yan na sa biyu da ɗan aikin gidan.”
Sai dai kuma majiyar bai shaida mana adadin kuɗaɗen da ‘yan bindigar ke neman a biya su kafin su saki Zulaiha da Zainab ba.
Discussion about this post