Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya yi kakkausan kira ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar cewa ya fito ya roƙi afuwa daga wurin sa, saboda ya kantara masa ƙarya.
A ranar Laraba ce Ortom ya yi wannan gargaɗin ga Atiku, lokacin da ya karɓi siyasar da ƙungiyar Matasan Jemgbagh su ka je yin zanga-zanga a Gidan Gwamnatin Jihar Benuwai, a Makurɗi.
Ortom ya ce Atiku ya nemi afuwar Ortom, saboda ya ce ‘yan ‘uwan Ortom su na satar wa Fulani shanu a Benuwai.
“Yayin da na ji bayanin sa a labarai, nan da nan sai na tura masa saƙon tes ta WhatsApp, nan take kuma ya ba ni haƙuri.
“Amma sai na ce ya fito ya nemi afuwa, amma ya yi ƙememe ya ƙi fitowa sarari ya nemi afuwa daga wuri na.
“To ni abin da na ke cewa, ba zai yiwu Atiku ya yi wa dattijo kamar ni tsirara a tsakiyar kasuwa ba, sannan mu je gida ya suturta ni a cikin ɗaki.
“Ya shirga min ƙarya, kuma ba zan taɓa lamuntar haka ba. Furucin da ya yi a kai na kalaman ƙiyayya ne,” inji Ortom.
Gwamna Ortom ya ce ba gaskiya ba ne da Atiku ya ce Ortom ɗin ya yi wa Fulani jam’u, ya ce dukkan su ɓatagari ne. Ortom ya ce bai taɓa cewa haka ba.
“Wasu Fulani da dama abokai na ne, kuma na riƙe su amana har ta kai cikin ɗakin kwana na ma sun taɓa shiga. Kuma ni ban taɓa korar Bafulatani ko ɗaya ba.
“Amma Fulani baƙi ‘yan ƙasar waje masu shigowa daga Mali, Mauritania da wasu ƙasashe, su ne ke yi wa mutanen jihar mu ta’addanci.
“Atiku ba ka yi wa mutanen Jihar Benuwai adalci. To ka sani dai Fulani su kaɗai ba za su iya sa ka ci zaɓe har ka zama shugaban ƙasa ba.” Inji Ortom.
Sai dai kuma Ortom ya ce duk da rikita-rikitar da ta dabaibaye PDP, zai yi bakin ƙoƙarin sa domin jam’iyyar ta lashe zaɓen 2023.
Discussion about this post