Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbar da amincewar sa ga sauyin fasalin naira da babban bankin Najeriya, CBN ya bijiro da shi.
A tsarin wanda gwamnan bankin ya bayyana, za a fara amfani da sabon kudin daga watan Disambar 2022, zuwa karshen watan Janairu da za a dakatar da tsoffin wanda suke a ajiye ba a canja su ba.
Gwamnan CBN, Godwin Emiefile ya ce gwamnati za ta sauya fasalin kuɗin ne domin tsaftace hadahadar kuɗi a kasar nan ta yadda waɗanda suka kwashe su ka boye ya zama musu jidali.
Emiefile ya ce ” Kashe 80 cikin 100 na kuɗaden Najeriya na hannun mutane ne, ba su bankuna, sannan a waje kuma mutane ba kuɗi a hannun su.
Hakan na nuna cewa an jibge su a wasu wurare ne ba su hannun jama’a ana amfani da su.
Shehu ya ce shugaba Buhari ya gamsu kar ka da hujjojin da babban bankin Najeriya ya bashi waɗanda sune dalilan da ya sa za a sauya fasalin naira.
Hujjojin sun haɗa farfaɗo da tattalin arzikin kasa, sannan kuma ra a samu daidaituwa waken tsananin hauhawar farashin kayayyaki da ke samu da kuma jabun kuɗi da suka mamaye kasa.
Sannan kuma Buhari ya ce wata uku da babban bankin Najeriya ya tsara bai yi kaɗan ba.
Masu sana’ar arziki da ayyukan kwarai basu da matsala, amma waɗanda suka tara kuɗaden haram suka boye su ne za su lula da kan su.
Mutanen da ke da kudin haram da suka binne su a gidajen su za su fuskanci kalubale da wannan sabon abu da za a yi, amma ma’aikata, da ƴan kasuwa ba za su fuskanci wata matsala ba ko kadan,” inji Buhari.
Sauya fasalin Naira da babban bankin Najeriya ya bijiro da shi ya jawo dogon sharhi da bayanai daga ƴan Najeriya jar da kasashen waje.
Discussion about this post