Da farko dai, tuni ‘jumhur’ na mutanen wannan ƙasar suka yanke hukunci a karan-kansu cewa “…komai ma a ƙasar nan zai iya faruwa; duk abinda ya faru a ƙasar nan ba abin mamaki bane…” sabida haka, fitar da shugaban wannan ƙungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu, daga Kotu tare da korar duk ƙararraki, ko kuma yin watsi da zarge-zargen da ake yi masa, shi ma ba abin mamaki bane.
Ko da yake sha’anin Kotu ne, kuma Bahaushe ya ce “shari’a sabanin hankali ce” ita – ban da haka, da na ragargaji wannan hukuncin, gaskiya. Sabida idan akwai abinda gwamnatin Nijeriya za tayi – wanda a gani na, bai kamata mutane su kawar masa da kai ba, to wannan ne.
Mutumin nan dai, na farko: daga mutanen Nijeriya har gwamnati, kowa ya gamsu shine shugaban ƙungiyar nan ta IPOB – wato masu rajin kafa haramtaccitar ƙasar Biafra. IPOB din nan kuma, ba malamai bane – yayan iska ne; masu kashe jama’a ba bu gaira; ba bu sabab. Shine ma yasa gwamnati da kan ta; ta ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda’.
Akwai shaidu sosai da suke nuna irin kyakkyawar alaƙa tsakanin mutumin nan da yan ta’addar nan – domin ko lokacin da aka kama shi, sun yi ta fadin maganganu iri-iri cewa sai an sake shi; sun yi taruka iri-iri – wanda a ƙarshe dai suka kama shi. Kuma yanzu kwatsam, ace an sake shi?
To ina labarin hukuncin kisan da mutanen sa suka yiwa mutanen Arewa basu ji ba; basu gani ba? Ina labarin hukuncin barnar da mutanen sa suka yiwa mutanen Arewa? Ni ina zargin cewa an yi wannan ne domin kwadayin samun ƙuri’un ƙabilar Igbo kawai. APC ba su da tunani. Ina labarin hukunci akan barnar da suka yiwa gwamnati na ƙone-ƙonen ofisoshin yansanda dana INEC da sauran jami’an tsaron da suka yi – banda ma kisan gillar da suka yiwa jami’an tsaron?
Ina labarin hukuncin daya kamata a yiwa mutanen sa, dangane da kafa dokar hana fita duk ranar Litinin da yaransa suka yi; da kashe duk mutumin daya bude kasuwa ranar; da kisan Fulani da Hausawa – ciki har da wannan matar Amina, wadda aka kashe ta da yaran ta su hudu – kuma har yanzu ba’a sake cewa komai ba? Ina duk wadannan labaran?
Yanzu ko shi kan sa laifin bayyana son raba ƙasa, bai isa ace gwamnati ta hukunta wannan mutumin ba ashe? Ba bu mamaki ma, gudun magana ne yasa gwamnatin Mai Gaskiya, Buhari, ya hana su – amma da tuni Nnamdi Kanu yana daga cikin nagari da bata garin mutanen da gwamnatinsa ta karrama a cikin makon nan da lambar girmamawa ta ƙasa. Gara ma su ƙara hada wani taron; su ba shi. Ko kuma su kai masa ita har gida.
Koda yake Abubakar Malami, Ministan Shari’a, bayan da mutane suka fara yin magana akan fitar dashi da gwamnatinsu tayi, yace wai “…ba sallamar sa akayi ba; fitar dashi kawai akayi…” wanda ‘wataƙila’ da mutane shiru suka yi; da bai sake jawabi ba. Tunda a ƙasar nan wane hukuncin son rai gwamnati take dauka; kuma har ta fito; tana yiwa yan ƙasa ƙarin haske?
Ta tabbata dai gwamnatin Buhari ‘hatta’ matsalolin data tarar kafin zuwan ta, sai ta barwa mai zuwa gadon su – bisa dukkan alamu, akwai siyasa a cikin wannan hukunci da suka yi – sabida kwadayin samun ƙuri’un ƙabilar Igbo a zaben shekarar 2023. Allah Yasa dai ba mummunar manufa ce, kamar yadda ake zargi, tasa gwamnatin Buhari ta saki mutumin nan ba!
Discussion about this post