Sojoji daga Rundunar Operation Delta Safe, wato Zaratan Jaddada Zaman Lafiya a Yankin Neja Delta, sun gano tare da lalata matatar ɗanyen man sata har guda 23, sannan kuma su ka kama ɓarayin ɗanyen mai 42 a cikin makonni biyu, a yankin Neja Delta.
Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Tsaro, Musa Ɗanmadami ne ya bayyana haka a Abuja ranar Alhamis, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai.
“Kuma sojoji sun yi sintirin kakkaɓe matatun ɗanyen mai na sata masu yawan gaske, tare da ragargaza su, kuma sun ragargaza tankunan tara mai da kwale-kwalen katako, murhunan hura wutar tace ɗanyen mai, ramuka da sauran su, duk an lalata su.
“Baki ɗaya dai a cikin makonnin biyu an samu nasarar gano matatun ɗanyen mai na sata guda 23, kwale-kwale 87, ƙananan jiragen ruwa masu gudun tsiya guda 7, tankunan ɓoye mai guda 284, sai kuma sauran kayayyakin da su ka haɗa har da murhunan dafa danyen mai domin tacewa.
“An ƙwato lita 133,824 ta dizal, sai kuma lita 7,000 ta kananzir
“Sannan kuma an ƙwato tankuna 16, tankar jirgin ruwa ɗaya, injin tunkuɗo mai 8 da babura guda biyu.
“An kuma samu nasarar kama ɓarayin ɗanyen mai gida 42.
Manjo Janar Ɗanmadami ya ce da kayan da aka ƙwato da ɓarayin da aka kama, duk sojoji sun damƙa su ga hukumar da ta dace.
Ya ce sojoji su na ci gaba da aikin sintiri na farautar ɓarayin ɗanyen man fetur masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa.
Ya ƙara da cewa sojoji a wani sintirin sun kama tamkar jirgin ruwa MT DEIMA, wadda za ta iya ɗaukar ɗanyen mai har ganga 1500.
Ya ce an kama shi ne a yankin Sara, ma’ajiyar Escaravos Channel a ranar 7 Ga Oktoba.
Discussion about this post