A ranar Asabar manyan ‘yan siyasar Najeriya biyu, kuma manyan masu takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu da Atiku Abubakar na PDP sun ci kasuwa a garin Kaduna.
Yayin da Tinubu ya halarci taron Bunƙasa Hannayen Jari da Cinikayya a Kaduna, shi kuwa Atiku ya gana da jama’a ne a Arewa House.
Kowanen su ya baje kolin siyasa da kamfen ɗin sa a ciki jawaban da su ka yi.
Sai dai kuma lamarin bai yi wa su biyun daɗi ba, domin kowanen su ya yi kwafsawar da ta janyo masa surutai da hantara a soshiyal midiya da sauran kafafen yaɗa labarai manya da ƙanana.
Katobarar Tinubu:
Yayin da Tinubu ke bai wa Gwamna Nasiru El-Rufai shawarar kada ya zubar da makaman siyasa a 2023 ya yi ritaya kamar yadda ya taɓa bayyanawa, Tinubu ya kwafsar inda ya yabi ayyukan raya ƙasa da El-Rufai ya yi, a ƙoƙarin yabon sa, sai ya ɓata rawar sa da tsalle.
“Ba za mu bari ka gudu daga siyasa ko mulki ba. Irin namijin ƙoƙarin da ka yi inda ka maida Kaduna ruɓaɓɓen birni zuwa ƙazamin birni, ya nuna cewa kai abokin tafiya ne…”
Kasassaɓar Atiku:
Shi kuwa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa Arewa ba ta buƙatar Bayaraben ɗan shugaba ko Inyamirin shugaba. “Wanda Arewa ke buƙata shi ne ɗan takara daga Arewa, wato ni, wanda ya yi gogayya da kowane ɓangare na ƙasar nan.”
Shi ma Atiku wannan kasassaɓar Atiku janyo masa tsangwama sosai. Dama kuma ga shi PDP na fama da rikicin cikin gida da su Gwamna Nyesom Wike da wasu gwamnoni huɗu masu goyon bayan Wike ɗin da ke cewa lallai sai dai Shugaban PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayu ya sauka a naɗa wani daga Kudu.
Gar-da-gar Ɗin Khalifa Muhammadu Sanusi II:
Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, tsohon Sarkin Kano kuma Shugaban Gidauniyar Bunƙasa Hannayen Jari da Cinikayya ta Kaduna, ya bayyana cewa duk wani ɗan takarar da ya ce gyaran matsalar Najeriya abu ne mai sauƙi, to maƙaryaci ne, ko kuma bai san matsalar da ke damun Najeriya ba.
Da ya ke magana kan lalacewa ko taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasa, ya ce ya zama dole idan ana so a ci gaba, to sai an tasa ƙaryar NNPC sun nuna yawan jiragen ruwan da su ka riƙa kawo fetur ɗin da aka riƙa fitar wa da kuɗaɗen tallafi.
Khalifa ya yi wannan bayani a gaban Tinubu, wanda ya ce idan ya hau mulki za a ci gaba a cikin gaggawa, kuma zai yi gyara sosai.
Discussion about this post