Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, kuma murabus Sarki Muhammadu Sanusi II na Kano, ya ce ya na tausayin shugaban da zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari, dangane da gagarimar matsalar tattalin arzikin ƙasa da zai fuskata, musamman matsalar tallafi fetur da kuma ɗimbin bashin da zai riƙa biya tilas a kowane wata.
Sanusi ya ragargaji NNPC, ya na mai cewa ba ta da wani amfani, ruguje ta kawai shi ya fi alheri.
Muhammadu Sanusi ya yi wannan bayani ne a Taron Bunƙasa Hannayen Jari da Kasuwanci na 7 na Jihar Kaduna, wato Kadinvest.
Ya ce ana amfani da sunan tallafin fetur wasu na azurta kan su a rana ɗaya, su na zama biloniyoyi.
“Cikin 2023, idan mu ka yi zaɓe, to bai yiwuwa fa a ci gaba da yadda ake tafiya a yanzu, saboda idan aka ci gaba da tafiya a haka, matsalar tsaro za ta sake ɓarkewar da ka iya kai mu ga halin da Mali da Burkina Faso ke ciki a yanzu.
“Bai yiwuwa mu ci gaba da ci gaban mai ginin rijiyar da babu alamar ruwa. Ya zama tilas mu dawo baya.
“A yanzu fa kuɗin da Najeriya ke samu a duk wata, ya na tafiya ne wajen biyan bashi.
“Da bashi Gwamnatin Tarayya ke ciyar da gwamnatin kuma da bashi ta ke gina titina, da bashi gwamnati ke biyan albashi da bashi kuma ta ke yin hidimomin tafiyar da gwamnati.
“Mu na barin gadon tulin bashi kan ‘ya’yan mu. ‘Ya’yan mu nan gaba za su iya tsine mana, saboda tulin bashin da ake ciwowa ana lafta wa maciya tallafin fetur kuɗin, su na watandar su hankali kwance.
“Mu na ganin wannan gagarimar matsala, amma kuma sai ci gaba da nausawa cikin ta mu ke yi mu na ninƙaya. Ina jin tausayin duk wanda zai zama shugaban ƙasa nan da watan Yuni, idan ya hau washegari gari ya ce zai cire tallafin fetur.”
Khalifan na Tijjnaniya ya ƙalubalanci adadin lita miliyan 66 da NNPC ya ce ake sha ta fetur a kullum a Najeriya, abin da hakan ke nufin cewa ana fitar wa lita miliyan 66 kuɗin tallafi kenan a kullum.
“Cikin 2019, mu na shigo da lita miliyan 40 a kullum ta fetur. Cikin 22 an ce ana shigo da lita miliyan 66 a kullum ta fetur. Hakan fa na nufin a cikin shekaru uku an samu ƙarin fetur ɗin da ake sha da kashi 50 cikin 100 kenan.
“Ina so don Allah a faɗa min, shin yawan jama’a ne ya nunka a cikin shekaru uku, ko kuwa yawan motocin da ake hawa ne su ka ƙaru har su ka nunka? Ko kuwa dai mu ma mutane fetur ɗin mu ke sha kamar yadda mu ke kwankwaɗar ruwan sanyi?
“NNPC ya ce mu na shan lita miliyan 66 a kullum. Kenan fa mun fi ƙasar Indonesiya da Pakistan da Egypt da Cote d’Ivoire da sauran ƙasashe shan fetur a kullum kenan.
“Abin da ya kamata wanda duk ya zama shugaban ƙasa ya fara yi idan ya hau a 2023, shi ne ya umarci NNPC ya kai masa shaida hujjojin dukkan maƙufan kuɗaɗen da aka ce an biya da sunan tallafin fetur. Tilas su bayar da sunayen jiragen ruwan da su ka ce sun kawo fetur ɗin. Kuma tilas mu je mu tabbatar daga kamfanonin inshorar jiragen, tunda duk mun san su. Kuma sai mun gano shin jiragen sun zo Najeriya a ranakun da ake rubuta sun zo ɗin?
“Abin da doka ta ce shi ne tilas sai ka tabbatar da fetur ɗin an shigo da shi a farashin da aka ƙayyade, kuma adadin ne aka shigo da shi daidai kafin ka fara kiciniyar biyan kuɗin tallafi.”
“A yanzu NNPC rijiya ce gaba dubu da ake zunduma kuɗaɗen Najeriya, su na salwanta a banza, maimakon a ce ta zama saniyar da Najeriya ke tatsa ta na samun nono da mai ta na sha, ta na kuma sayarwa.”
Sanusi ya nuna damuwa cewa Gwamnatin Tarayya za a samu dala biliyan 2.9 ne kaɗai daga fetur a wannan shekarar, ba kamar 2011 ba da aka samu har dala biliyan 60.
Discussion about this post