Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN, Kingsley Moghalu, ya tsoma ƙafar sa cikin rikita-rikitar canjin kuɗi da ta dabaibaye ƙasar nan a halin yanzu.
Moghalu wanda ya sha fitowa takarar shugabancin Najeriya, ya bayyana cewa babu inda doka ta ce don Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) zai canja kuɗi, tilas sai ya sanar da Ministar Harkokin Kuɗaɗe.
Moghalu ya ce CBN zaman kan sa ya ke yi, kuma cin gashin kan sa ya ke yi a matsayin sa na rumbum adanawa da kula da kuɗaɗen Najeriya.
“Matsawar dai Godwin Emefiele bai karya dokar Najeriya batun canjin kuɗi ba, to ba sai ya sanar da Ministar Harkokin Kuɗaɗe ba.
“Saboda haka maganar ma sai ya jira ya nemi izni daga Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe ba ta ma taso ba kwata-kwata.
“A na tilas shi ne ya sanar da Shugaban Ƙasa, kuma ya sanar masa ɗin, har ma shi Shugaba Buhari ya goyi bayan a canja kuɗin. Shikenan ai magana ta ƙare.
“Abu na biyu shi ne ya zauna ya sanar da Kwamitin Gwamnonin CBN. Wannan kwamitin kuwa ya ƙunshi mutum 5, waɗanda su ka haɗa da shi kan sa Emefiele, sai Mataimakan Gwamnan CBN su huɗu. Akwai kuma wasu manyan jami’an CBN su 5, sai kuma wasu mambobi 7 daga waje, waɗanda su ka haɗa da Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe.
“To shi Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe aikin sa wakilcin Ministar Harkokin Kuɗaɗe da kuma ma’aikatar baki ɗaya. Shi ne zai riƙa kai wa Ministar Harkokin Kuɗaɗe bayanan dukkan abin da Kwamitin Gwamnonin CBN ya tattauna.
“Ni ban san kowane Babban Sakataren a yanzu ba. Shin ya sanar da Minista, ko bai sanar da ita ba, wannan kuma daban. Aikin sa ne dai ya sanar da ita, ba aikin Gwamnan CBN ba.” Inji Moghalu.
Dalilan Da Su Ka Sa CBN Ke Son Canja Launin Naira:
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya shirya ƙaddamar da sabunta takardun naira, a ranar 15 Ga Disamba, 2022.
CBN ya ce zai canja launin takardun kuɗin ne domin ya yi wa kuɗaɗen da ke hannun jama’a talala, sannan kuma ya taka wa tsadar rayuwa burki.
Wani dalilin kuma da CBN ya bayar, shi ne za a canja wa kuɗaɗen launi ne domin a magance babbar matsalar yawaitar kuɗaɗen jabu.
CBN dai ya yi shirin sauya launin takardar Naira 100, Naira 200, Naira 500 da kuma Naira 1000.
Sabbin kuɗaɗen za su fara shiga hannun jama’a a cikin Disamba. Daga nan kuma a cikin Janairu, 31 Ga wata, 2023 za a daina amfani da tsoffin da a yanzu ke hannun jama’a.
Yayin da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ke wa manema labarai bayani a ranar Laraba, ya ce CBN ya sha fama da ƙalubale daban-daban, wanda ya zama barazana ga martabar CBN da martabar Najeriya baki ɗaya.
“Matsalolin da ƙalubalen sun haɗa da kimshe maƙudan kuɗaɗe da jama’a ke yi ba tare da ana juya su ba.”
Ya ce an gano cewa kashi 85% na kuɗaɗen da ake jalautawa a hannun jama’a ba su shiga asusun CBN.
“Ya zuwa cikin watan Satumba,2022, alƙaluman ƙididdiga sun tabbatar da cewa naira tiriliyan 2.73 daga cikin naira tiriliyan 3.23 ɗin da ke juyawa a hannun jama’a, ba su cikin rukunin talalar bankunan ‘yan kasuwa, wato duk su na hannun jama’a.
“Sannan kuma hujjoji sun tabbatar da cewa hakan ya na ƙara haifar da tsadar rayuwa da tsadar kaya, lamarin da rabon da a samu hauhawar farashi sosai kamar bana, tun shekaru 17 da su ka wuce.
Ya kara da cewa ana samun yawaitar ruɓaɓɓu da rududdugaggun kuɗaɗe a hannun jama’a. Kan haka ne ya ce ƙarancin takardun kuɗaɗe masu kyau, marasa datti na rage wa CBN kwarjini. Sannan kuma ya na haifar da tangal-tangal ga tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce sauya launin takardun nairori zai rage yadda ake kinkimar maƙudan kuɗaɗe buhu-buhu ana kai wa masu garkuwa domin biyan diyya.
Sai dai kuma tuni jama’a sun shiga damuwa da ruɗani, musamman idan su ka tuna irin bala’in da aka fuskanta, cikin 1984 lokacin mulkin Buhari na soja, lokacin da aka yi canjin kuɗi.
Discussion about this post