A ranar Laraba ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ta roƙi Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) da Gwamnatin Tarayya cewa mafi alheri ga ɓangarorin biyu shi ne su fita waje su sasanta junan su da kan su.
Ɗaya daga cikin alkalai ukun da ke sauraren shari’ar mai suna Biobele Georgewill ne ya yi wannan roƙon ga lauyoyin ɓangarorin biyu.
“A matsayin ku na manyan lauyoyi, mafi alheri ga ɗaliban da ke zaman dirshan a gida da kuma mafi alheri ga gwamnati da ASUU, shi ne ku lauyoyin su ku je ku sasanta kan su a waje, ba a kotu ba.” Haka ya shaida wa lauyan ASUU, Babban Lauya Femi Falana da kuma lauyan Gwamnatin Tarayya, Babban Lauya James Igwe.
Femi Falana ne dai ya shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara, a madadin ASUU, inda ya ƙalubalanci hukuncin Babbar Kotun Tarayya, wadda ta umarci ASUU cewa ta janye yajin aiki, idan aka ci gaba da karatu, sai a ci gaba da tattaunawa tsakanin kungiyar da Gwamnatin Tarayya.
Yanke hukuncin ke da wuya sai ASUU ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara, ta ce ba ta gamsu da hukuncin Babbar Kotun Tarayya ba.
A ranar Alhamis ce za a ci gaba da sauraren ƙarar. Sannan kuma za a zuba ido a ga ko ɓangarorin biyu za su janye daga kotu, su sasanta junan su.
Sai dai kuma, yayin da ake rigimar a kotu, PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Gwamnatin Buhari ta yi wa ƙungiyar ASUU kishiyoyi biyu a rana ɗaya.
Gwamnatin Tarayya ta yi wa sabbin ƙungiyoyin malaman jami’o’i biyu rajista, a yunƙurin gwamnatin na karya lagon ASUU.
Ƙungiyoyin biyu a aka bai wa katin shaidar rajista sun haɗa da NAMDA, wato Medical and Dental Academic da kuma CONUA, wato Congress of Nigerian University Academics.
Ministan Ƙwadago Chris Ngige ne ya damƙa wa shugabannin ƙungiyoyin satifiket a ofishin sa, a ranar Talata.
Ƙirƙiro sabbin ƙungiyoyin malaman jami’o’in biyu dai wani yunƙuri ne da gwamnati ta yi domin karya ASUU, ƙungiyar da mambobin ta ke yajin aiki tsawon watanni takwas kenan.
“Waɗannan ƙungiyoyin za su ci gaba da wanzuwa su na gudanar da harkokin su kafaɗa da kafaɗa da ASUU,” haka Ngige ya bayyana yayin da ya ke jawo wasu ayoyi daga cikin Kundin Dokar Aikin Ƙwadago ta Kungiyar Kare ‘Yancin Ma’aikata ta Ƙasa da Ƙasa (ILO), wato International Labour Organization, Sashe na 87 da na 98, wanda ya ce sassan biyu ne su ka bayar da ‘yancin kafa ƙungiya ga duk wani rukuni ko gungun da ke buƙatar yin haka.
Ngige ya shawarci sabbin ƙungiyoyin biyu kada su riƙa shiga sharo ba shanu cikin harkokin hukumar gudanarwar jami’o’in da su ke koyarwa a ciki.
Ya ce jajircewar da ASUU ta yi cewa tilas sai dai a riƙa biyan malaman jami’o’i albashi bisa tsarin UTAS, katsalandan ne ƙungiyar ta yi a cikin ‘yanci da haƙƙin da doka ta bai wa wanda ya ɗauki ma’aikaci aiki.
“Ai ya kamata kai da aka ɗauka aiki ka fara mutunta ‘yanci da haƙƙin wanda ya ɗauke ka aiki, kafin shi wanda ya ɗauke ka ɗin ya mutunta ‘yanci da haƙƙin ka.”
A taƙaice Ngige na ƙoƙarin nuna cewa bai yiwuwa gwamnati ta ɗauki mutum aiki, sannan kuma ya ce shi zai kafa mata dokar yadda ya ke so ya yi mata aikin.
“Kada ku malaman jami’o’i ku riƙa shiga harkokin hukumar gudanarwar jami’o’in ku. Misali, babu ruwan mu da shiga siyasar wanda zai zama shugaban hukumar gudanarwar jami’a ko Shugaban Jami’a (Vice-Chancellor).
Haka nan Ngige ya sanar da sabbin ƙungiyoyin cewa hukumar gudanarwar kowace jami’a ba za ta shiga cikin sha’anin zaɓen shugabannin sabbin ƙungiyoyin na malaman jami’a ba, kamar yadda kundin tsarin dokokin ƙungiyoyin ya gindaya.
Kafa Ƙungiyoyin sabbi guda biyu ya biyo bayan kika-kakar da ake ta fama tsawon watanni da dama tsakanin Minista Ngige da Shugaban ASUU, Emmanual Osodeke.
Discussion about this post