Cikin watan Satumba Sojojin Sama sun kai harin bama-bamai a sansanin ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Kachalla Turji. Wani bidiyon da aka nuno bayan harin an ga Turji na magana cikin ɓacin rai, ya na cewa harin da aka kai masa karya yarjejeniya ce ta rungumar zaman lafiya da ya ƙulla da gwamnati.
Haka nan kuma harin bama-baman ya yi saɓani da iƙirarin da Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara ya yi cewa “Turji ya rungumi yarjejeniyar zaman lafiyar da ya ƙulla shi da gwamnatin jihar.”
Maganar gaskiya ita ce, Turji dai ya aika mumnunan ta’addancin da ya kamata a ce an hukunta shi. Sai dai kuma wannan matsala ta ƙara faɗaɗa tunanin kallon da ake yi wa matsalar tsaro a ƙasar nan.
Ana samu rashin aiki tare, rashin tuntuɓar juna ko kuma yin gaban-gabarar wani ɓangare na tsaro ko gwamnati, ba tare da tuntuɓar wani ɓangaren da ya zama wajibi a tuntuɓa kafin aiwatar da waɗansu hare-hare ko farmaki kan masu tayar da fitina ba.
Babban misalin irin haka shi ne wasiƙar da Mashawarcin Tsaron Shugaba Muhammadu Buhari, wato Babagana Monguno wanda ya rubuta wa Shugabannin Sassan Tsaro cikin Fabrairu, 2020.
Wasiƙar na fito da saɓani da rashin jituwar da ke tsakanin sa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa na lokacin, Abba Kyari.
Mu ɗauki sakacin yadda aka sace ɗaliban sakandaren Dapchi a Jihar Yobe, farmakin Kurkukun Kuje da farmakin jirgin ƙasa mai ɗauke da fasinjoji. Lamarin ƙarara ya nuna tsarin tsaron ƙasar nan tamkar matacce kifi ne, wanda ya ke fara ruɓewa daga kan sa.
Shugaban Ƙasa na bakin ƙoƙarin sa wajen iya ƙulle-ƙullen siyasa, amma kuma ya yi shakulatin-ɓangaro da matsalar tsaro. Babu komai sai yawan nanata alƙawarin kawo ƙarshen matsalar tsaro, wanda ci gaba da hakan ba tare da ganin biya bukata ko samun zaman lafiya a ƙasa ba, hakan na nuni da rashin sanin makamar aiki ce ɗungurugum.
Tsakanin gwamnati da ɓangarorin tsaro kowa alƙiblar da ya fuskanta daban da ta saura. Misali, babu kyakkyawar sadarwa tsakanin dakarun da ke filin daga da kuma hedikwatar su. Haka danganta tsakanin ɓangarorin tsaro ba ta da danƙo sosai. Da wahala ɗaya ɓangaren ya san abin da ɗayan ke shirin aikatawa.
Haka lamarin ya ke tsananin gwamnatin jiha da Gwamnatin Tarayya kan batun tsaro, kowa tsagin da ɗauka daban, kuma kowa ba ya neman shawarar ɗaya ɓangaren.
Dokar Najeriya ta 1999 ta fayyace wanda ke da alhakin kula da ‘yan sanda da sojoji. Har yau gwamnatin tarayya ta ƙi amincewa a samar da ‘yan sandan jihohi. Saboda haka ita ce ke da laifin maida rayuwar ‘yan Najeriya ta zama mai arhar da kisan jama’a ya zama ruwan dare a kullum.
Sannan akwai matsalar yadda gwamnati ba ta nuna jin tausayin iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su.
Irin yadda gwamnatin Buhari ta riƙa dukan ƙirjin wai ta yi bajinta, sojoji sun ceto sauran ragowar fasinjojin jirgin ƙasa su 23, abin takaici da abin kunya ne. Hakan ya nuna yadda aka kasa yin komai tsawon watanni shida a baya. Kuma tun da farko, da wannan gwamnatin ta ɗauki matakan tsaro yadda ya kamata, to da tun farko ba a yi garkuwa da fasinjojin ba.
Rashin iya tafiyar da al’amurran tsaron ƙasar nan yadda ya kamata, ya jefa dubban jama’a hannun masu garkuwa da mutane.
Babban abin takaici ne a ce Shugaban Ƙasa zai bar mulki bayan shafe shekaru takwas, ba tare da ya samu galabar daƙile matsalar tsaron da ya yi ta ɓaɓatun zai daƙile ba idan ya zama shugaban ƙasa, a tsawon shekaru 16 da ya shafe ya na neman mulki.
Amma dai a yadda ake tafiya yanzu, gwamanti na nuna kan ta cewa idan ta sauka, za a riƙa tunawa cewa ita ce ita ce wadda hususan ta bayar da ƙofar taɓarɓarewar Najeriya.
Discussion about this post