Iƙirarin da Buhari ya yi kwanan nan ya na cewa ya cika wa ‘yan Najeriya burin su, hakan ya nuna cewa Shugaban Ƙasa ya yi nesa sosai daga sanin haƙiƙanin halin ƙuncin da ‘yan Najeriya ke ciki. Yayin da rayuwa ta yi tsanani ga jama’ar da ɗaliban jami’o’in cikin su su ka shafe watanni takwas a gida saboda yajin aikin malaman su, a haka ɗin duk wanda ka kalla sau ɗaya za ka ga cewa akwai bajo na ƙuncin rayuwa, damuwa da baƙin rai a fuskar sa. Waɗannan halaye ne ke tabbatar da cewa soki-burutsu ne kawai Buhari ke yi, kuma dama irin kalaman da ya ke furtawa, haka gwamnatin ta sa ta ke.
Tun da ya hawo mulki a duk shekara tatsuniyar gizo ba ta wuce ƙoƙi. Ko kwanan nan a Taron Bibiyar Ayyukan Ma’aikatu na shekara-shekara, an tattauna batun “Inganta tsaro, yaƙi da cin rashawa da kuma haɓɓaka tattalin arzikin ƙasa.” Sai dai kuma idan aka ɗora wannan uku a kan sikeli, za a ga sun zama tatsuniya ba haƙiƙanin gaskiya ba.
Gaggan masu hana Najeriya zaman lafiya na nan daram su na ci gaba da aikata dukkan ta’addancin da su ke yi a cikin ƙasa. Boko Haram, ISWAP, mahara, ‘yan bindiga da makiyaya masu kashe mutane sun kai Najeriya a matakin ƙasa ta biyu a duniya inda aka fi ta’addanci.
An kashe ‘yan Najeriya 53,418 tsakanin 29 Ga Mayu, 2015 zuwa watan Oktoba, 2022 a kan idon Shugaba Buhari, kamar yadda Cibiyar Ƙididdigar Alƙaluman Kashe-kashe ta Nigerian Security Tracker ta tabbatar.
A yanzu haka mazauna Abuja na kwana cikin firgici sanadiyyar rahoton gargaɗin da ofishin jakadan Amurka da Birtaniya su ke yi cewa akwai yiwuwar ‘yan ta’adda su kai hari a babban birnin Najeriya, irin wanda su ka kai a Kurkukun Kuje, wanda su ka kuɓutar da ɗaurarru sama da 800, cikin su har da riƙaƙƙun kwamandojin Boko Haram. Babban abin ban-haushi a farmakin na Kurkukun Kuje, shi ne an aika wa gwamnatin tarayya rahoton sirri kan yunƙurin kai harin, amma ba ta yi komai ba duk kuwa da cewa sau 44 ana sanar da ita cewa akwai yiwuwar kai hari a kurkukun.
Irin yadda ake fallasa harƙallar da ke faruwa a cikin hukumomin yaƙi da rashawa ya nuna yadda jami’an da Buhari ke naɗawa su ma su ke shiga cikin harƙallar dumu-dumu.
Irin yadda jami’an gwamnatin Buhari ke afkawa cikin harƙalla abin takaici ne. Watannin baya Shugaban Hukumar Kwantan ta Ƙasa, Hameed Ali ya shaida wa Majalisar Tarayya cewa iƙirarin da NNPCL ya yi cewa an kashe naira tiriliyan 6 wajen biyar tattalin fetur cikin 2022, harƙalla ce kawai.
Har yanzu kuma Buhari a matsayin sa na Ministan Harkokin Fetur, ya kasa bayar da amsar wanzan zargi na Hameed Ali.
E, za ta yiwu Shugaba Buhari ya gina titina masu jimlar tsawon kilomita 3,800, ya gyara wasu titinan da ya ce sun kai 21 masu tsawon kilomita 1,804. Kuma ya kammala ginin Gadar Kogin Neja da ma wasu ayyukan da dama.
Sai dai kuma abin da Buhari ya yi ƙememe ya ƙi faɗi shi ne dukkan waɗannan tituna hawan su kasada ne. Ko dai a tare kashe mutum, ko a yi garkuwa da shi a biya maƙudan fansar da har naira miliyan 100 ake karɓa a hannun masu hali da shuni a matsayin kuɗin fansa.
Domin ko mutanen farko da aka yi garkuwa da su a cikin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna, sun biya diyyar jimlar naira 800 a cikin Yuli, 2022. A cikin watan ne aka kai wa tawagar Buhari farmaki kan hanyar su tafiya hutun Sallah zuwa Katsina, amma Buhari ba ya cikin tawagar a lokacin. Kuma a cikin watan ne aka buɗe wa Zaratan Sojojin Gadin Shugaban Ƙasa wuta a Bwari, Abuja.
Harkar ɗanyen mai ta shiga gargarar da a zamanin wannan gwamnatin ana yaƙo har ƙasa da ganga miliyan ɗaya, maimakon miliyan 1.830 da OPEC ta ce a riƙa haƙowa a kullum. Shi ya sa a kullum babu abin da wannan gwamnatin ta fi iya ci ta cika ciki fal sai tulin bashi.
Irin yadda ake satar ɗanyen man Najeriya abin mamaki ne a ƙarƙashin wannan gwamnati. Saboda haka gwamnatin da ke iƙirarin ta cika wa talakawan Najeriya burin su, ai ba za ta riƙa yi wa matsalar barayin ɗanyen mai riƙon-sakainar-kashi ba. Wannan lamari na rashin ɗaukar matsalar da muhimmanci ne ya sa PREMIUM TIMES ta bi sahun gwamnatocin baya tun daga 1999, wajen ƙin hukunta ɓarayin fetur.
Jama’a a kullum su na cikin tsadar rayuwa, har basu son kullum ana yi masu ƙididdigar alƙaluman tsadar abinci.
Abubuwan sun yi wa talakawa yawa, a ciwo bashi, ga tsadar rayuwa, ga giɓin kasafin kuɗi, ga zubewar darajar naira, inda yau ta kai har naira 781 ake sayen Dalar Amurka 1 tal, dalar da a 2014 kafin Buhari ya hau mulki, naira 180 ake sayar da ita a kasuwar ‘yan canji.
Discussion about this post