Ɗan takarar gwamnan jihar Abia na jam’iyyar PDP, Sampson Orji ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi ya fi Atiku Abubakar na PDP sau Dubu.
Sampson ya ce ” Zan yi wa Peter Obi aiki na babu kafar yaro duk da ina ɗan PDP kuma jigo kuma ma ɗan takarar gwamna a jiha ta, amma Obi zannyi wa aiki a takarar shugaban kasa.
” Da ni da iyalali na dukkan su za su zaɓi Obi ne. Da ma kuma ɗan yankin Kudu Maso Gabashin Kasar nan bai taba yin mulki ba, wannan da ma ce mula samu.
” Me nene yasa shi Atikun bai mara wa Obi baya ba, duk da cewa shine ya yi masa takarra mataimaki a zaɓen 2019. Ai da shima yanzu sai ya mara masa baya.
” Ni fa gaskiya ce zan fayyace ta ƙarara, shekaru 16 da PDP ta ke mulki a Najeriya, har yanzu hanyar Aba-Port Harcourt Expressway ba ka iya bi saboda muni.
” Ba ka isa ka bi hanyar Umuahia – Ikot Ekpene – Owerri – Umuahia saboda nan ma ya dagargaje kuma mulkin PDP bata yi komai a kai ba. Saboda haka ni ba makaho bane. Obi ya fi cancanta, ya fi kwarewa sannan ya fi zama wanda aya dace mu bi don nasara a zaɓe mai zuwa.
Discussion about this post