Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta bada umarnin a kulle Masana’antar Dangote Cement, bisa dalilin wasu zarge-zarge da ƙorafe-ƙorafe da ake yi.
A ranar Laraba ce Majalisar Dokokin ta bayar da umarnin, biyo bayan wasiƙar ƙorafin da mazauna Obajana, garin da kamfanin ya ke, su ka rubuta wasiƙar ƙorafi.
Majalisa ta kira Ɗangote, wanda shi ne na mafi karfin arziki a Afrika, domin ya je ya bayar da ba’asi, amma ya nemi a bayar da isasshen lokaci.
PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Kakakin Ɗangote Cement PLC, Anthony Chiejina, amma bai maida amsar saƙon tes da wakilin mu ya yi masa ba.
Mazauna yankin dai sun rubuta wasiƙar ƙorafin cewa ana ɓata masu muhalli, kuma ba a inganta rayuwar al’ummar yankin, kamar yadda doka ta wajabta wa masana’antar, kasancewa a yankin ne ta ke samun biliyoyin kuɗaɗe a duk shekara.
Ƙorafin da mazauna yankin su ka kai ya tayar da bincike ƙwaƙwaf ɗin da Majalisar Kogi ta ce ta gano cewa Ɗangote Cement ya sayi kamfanin daga Jihar Kogi tun cikin 2002, ba tare da ƙwararan takardun cinikayya ba.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kogi, Kingsley Fanwa ne ya sanar da manema labarai haka.
Dalili kenan Majalisa ta bada umarni a kulle masana’antar, har sai an gabatar mata da takardun ciniki.
Dangote Cement ya sayi kamfanin simintin daga hannun Jihar Kogi cikin 2002, a lokacin da ake kiran sa da suna Obajana Cement Company.
Ɗangote Cement a yanzu shi ne masana’anta mafi tsada ta biyu a Najeriya.
Cikin 2022 tsakanin Janairu zuwa Yuni kamfanin ya yi cinikin siminti na naira biliyan 808, wanda a ciki naira biliyan 172.1 duk riba ce ta watanni shida.
Discussion about this post