Hukumar EFCC ta kama wani tantirin ƙasurgumin ɗan harƙalla da safarar ƙwayar Tramol a Najeriya.
Kakakin hukumar Femi Babafemi ya bayyana a wata sanarwar cewa hukumar ta kama Ugochukwu Chukwukadibia shugaban kamfanin motocin na Autonation Motors Ltd, da rumbun damin kayar tramol da kuɗin sa ya kai naira biliyan 8.8.
” An kama kwayoyin tramol sama da miliyan 13 dankare a gidan Ugochukwu, wani ƙasurgumin attajiri da ke zama a Lekki, jihar Legas, da kudin su suka kai naira biliya. 8.8.
Wannan kamu da EFCC suka yi ya zo kwanaki kaɗan bayan hukumar ta cafke wani ƙasurgumin dan harƙallar kwayoyi da shi kusan masana’anta ce a ya ke da ita sukutum na sarrafa kwayoyin dabandaban a cikin gidan sa, da kuma wata katafaren shagon siyar da magani.
Bincike da aka gudanar kafin a damke Ugochukwu ya nuna yana da dankara-dankaran gidaje masu a VGC dake Legas, kuma a cikin ɗaya ne yaka buga harkallar kwayoyinsa na tramol.
Shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai murabus, ya ji n jina wa kwazon jami’an hukumar bisa wannan babban kamu da suka yi.
Idan ba a manta ba, a cikin makon jiya hukuma ta damke wasu mashahuran masu safarar hodar ibilis na kasa da kasa a jihar Legas.
Bayan tantance kwayoyin da kama, hukumar ta kona su kaf din su da aka yi musu kuɗi naira biliyan 198.
Discussion about this post