Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya hori ƴaƴan Jam’iyyar APC da su dunƙule wuri guda domin n samun nasarar jam’iyyar APC a zaben 2023.
Hakan na kunshe ne a cikin jawabin da shugaba Buhari ya yi a wurin tarin ƙaddamar da ɓangaren mata na kamfen ɗin ɗan takarar shugaban kasa Bola Tinubu da aka yi a fadar shugaban kasa dake Abuja
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Kasa, Ibrahim Gambari ne ya wakilci shugaba Buhari a wurin taron.
“Don haka ina kira ga daukacin mambobin wannan kwamiti da su dauki wannan gagarumin nauyi a matsayin wani abu na sadaukar da kai ga jam’iyyar APC a wannan lokaci da kamfen ya kunno ka
“Ina da yakinin cewa wannan kwamiti zai kai jam’iyyar APC zuwa ga kololuwar nasara ta hanyar bunkasawa da aiwatar da dabarun hadakan jam’iyyar don tabbatar da nasarar ta a zaben 2023 domin babu wata hanyar da ta wuce nasararmu.
Sai dai kuma shugaba Bihari ya yi gargadi da yin kira ga Kungiyar cewa lallai aikinsu ya tabbata ya hada da zagaya ɗaukacin kananan hukumomin ƙasar nan 774, su tallata Jam’iyyar da kuma samun goyon bayan mutane a karkara.
Saboda haka kada a tattare a Abuja gaba ɗaya da sunan wai ana kamfen, a yi watsi da mutane a karkara.
A ƙarshe, ya umarci su mata da su baiwa Jam’iyyar da ɗan takarar ta , Bola Tinubu iri nbgoyon bayan da suka ba shi a baya domin samun nasara a zabe na zuwa.
Discussion about this post