Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya jaddada cewa ya yafe wa Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, saboda tsayawa takarar zaɓen fidda gwani da ya yi tare da shi.
Tinubu ya ce bai ƙullaci Osinbajo ba, kuma ba ya kwana da haushin sa.
“Wanda zai roƙi Allah gafara domin ya yafe masa zunubai, to shi ma ai tilas ya yafe wa wani. Saboda haka na yafe wa Osinbajo, ba ni kwana da haushin sa, kuma ban ƙullace shi ba.
“Kuma idan ba a manta ba, ai bayan na yi nasara a zaɓen fidda gwani, na je har gidan sa mun gana.
“Sannan kuma a lokacin Taron Bitar Ministoci, mun gaisa, mun tattauna batutuwa a wurin.
Tinubu ya yi waɗannan bayanai ne a ranar Litinin a Kano, lokacin da ya ke ganawa da gungun magoya bayan Osinbajo a lokacin zaɓen fidda-gwani.
Kodinetan Drone Marshall Support Group mai suna Alwali Hassan, ya roƙi TInubu ya rungumi Osinbajo da sauran waɗanda ya kayar a lokacin zaɓen fidda-gwani, domin a samu nasarar lashe zaɓen 2023.
Osinbajo dai yaron Tinubu ne, ya yi masa Kwamishinan shari’a daga 1999 zuwa 2007, lokacin da Tinubu ɗin ke Gwamnan Legas.
Ana kyautata zaton kuma Tinubu ya bayar da sunan Osinbajo aka zaɓe shi mataimakin takarar shugaban ƙasa na Muhammadu Buhari a APC, cikin 2015.
Discussion about this post