Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya lashi takobin kawo karshen yuwa, fatara da talauci a Najeriya idan ya zama shugaban kasa.
Atiku ya faɗi haka a lokacin da yake ƙaddamar da kamfen din sa a garin Uyo babbar birnin jihar AkwaIbom.
” Yau muna ƙaddamar da kamfen ɗin mu na takarar shugaban kasa mai taken, ceto Najeriya daga tsananin talauci, yunwa da kuma tabbatar da haɗin kai tsakanin ƴan kasa baki ɗaya.
” Idan kuka zaɓi PDP, kun zaɓi jam’iyyar da za ta kawo karshen talauci da yunwa kwatakwata, sannan kuma za a samu haɗin kai da ƙarshen ta’addanci gaba ɗaya.
” Na rantse idan kuka zaɓi PDP a 2023, za ku koma makaranta, kuma kowa zai samu aikin yi.
Lokacin da PDP ta kafa gwamnati a Najeriya a 1999, kowa ya shaida, tattalin arziki ya bunƙasa, an samu walwala da cigaban arziki, amma tun zuwan APC a 2015, abubuwa suka tabarbare.
Tun daga ƙarshen watan Satumba, aka buga gangar soma Kamfen a faɗin ƙasar nan.
Jam’iyyu gaba daya kaf ɗin su sun fantsama cikin ruguntsimin neman ƙuri’un ƴan Najeriya, tun daga kauyuka har zuwa birane.
A babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, a ranar Litinin an ƙaddamar da kungiyar mata magota batan ɗan takarar shugaban Kasa na APC wato Bola Tinubu.
A wurin ƙaddamar da kwamitin, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya hori ƴaƴan jam’iyyar su tabbata sun zagaye kauyuka da biranen kasar nan kafa domin karkato da ra’ayoyin mutanr su zaɓi jam’iyyar APC.
Discussion about this post