Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto, Muktar Shagari, ya bayyana cewa an yi masa tayin yi wa Peter Obi takarar mataimakin shugaban ƙasa, amma ya ƙi amincewa da karɓar tayin.
Cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels, ya ce tabbas tun da farko wasu jiga-jigan jam’iyyar LP sun runtuɓe shi domin ya zama mataimakin takarar shugaban ƙasa ga Peter Obi, amma bai amince ba.
A yanzu dai Datti Ahmed ne daga Jihar Kaduna ya ke ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Peter Obi.
“Tabbas da farko ni wasu manyan jam’iyyar LP su ka fara tuntuɓa don na zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a LP. Amma da na yi nazari da zurfin tunani, sai na ga babu yadda za a yi Peter Obi ya yi nasara a zaɓen 2023.
“Peter Obi ya na da magoya baya, amma duk ‘yan taratsi ne kawai a soshiyal midiya. Idan ka baje siyasar ƙasar nan a faifai, ai ba ma sai an yi maka ƙarin haske ba. Kai da kan ka za ka bai wa kan ka amsar cewa LP ba za ta iya yin nasara ba,” Inji Shagari, wanda ya taɓa yin Ministan Harkokin Noma a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo.
“Idan batun cin zaɓe ne, to duk wanda ya san siyasa sosai zai gaya maka cewa sai dai ko a APC ko PDP, cikin su ɗaya ce za ta yi nasara. Ɓata lokaci ne ma a tsaya ana maganar wata LP idan ga APC da PDP.
Yayin da a soshiyal midiya da kuma wasu sassan kudancin Kudu maso Gabas Peter Obi ya samu karɓuwa, har yau ba shi da wani tasiri a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, inda nan ne yankunan da su ka fi masu jefa ƙuri’a da ɗimbin yawa.
Haka kuma a Arewa ana yi wa LP kallon wata jam”iyyar da masu goyon bayan IPOB, wato tsagerun ƙabilar Igbo.
Peter Obi dai shi da Kwankwaso na NNPP duk daga PDP su ka ɓalle neman takarar shugaban ƙasa a wasu jam”iyyu daban da PDP.
Shi ya sa masu nazari da sharhin siyasa ke kallon cewa fitar su Obi daga PDP ya rage wa jam’iyyar yawan magoya ba, musamman magoya bayan Rabi’u Kwankwaso, masu jajayen huluna.
Discussion about this post